An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra'ila da Hezbollah
- Amurka ta sanar da cewa Isra'ila ta cimma matsayar tsagaita wuta da mayakan Hezbollah da ke Kudancin Lebanon
- An yi nasarar cimma matakin ne bayan shafe sama da shekara guda ana musayar wuta inda Isra'ila ta rike wuta
- Shugaban Amurka, Joe Biden ga bayyana cewa za a samu tsagaita wuta na tsawon watanni biyu, kafin daina yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Israel - A yau Laraba ne aka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hezbollah masu fafutukar kare kasarsu.
Wannan zai kawo saukin kazamin yakin da sojojin Isara'ila ke kaddamarwa a kan iyakar Lebanon-Isra'ila na sama da shekara guda.
AP News ta wallafa cewa har yanzu ana shakkun ko za a tabbatar tare da mutunta yarjejeniyar da ke da raunin gaske.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka ta sanar da cimma tsagaita wuta
BBC ta wallafa cewa shugaban kasar Amurka mai barin gado, Joe Biden ne ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60.
A wannan lokaci ne dakarun Isra'ila za su janye daga Kudancin Lebanon, yayin da sojojin kasar Lebanon za su mamaye wuraren da Hezbollah ke da karfin iko.
Isra'ila ta yi martani kan tsagaita wuta
A martanin shugaban kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce sojojinsa ba za su bata lokaci ba matukar Hezbollah ta saɓa yarjejeniya.
Kawo wannan lokaci ba a ji martanin kungiyar Hezbollah kan yarjejeniyar ba, amma ba a samu wata alama ta karya abin da aka cimma na tsagaita wuta ba.
Kasar Isra'ila za ta tsagaita wuta da Lebanon
A baya kun ji cewa kasar Isara'ila ta fara shirin tsagaita wuta da Lebanon bayan shafe sama da shekara guda ta na kai munanan hare-hare a Kudancin kasar.
Wakilin Amurka, Amos Hochstein da ke jagorantar tattaunawa don cimma tsagaita wuta ya bayyana fatan za a kawo karshen yakin da zubar da jini da ake yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng