Sojojin Nijar Sun Dora a kan Aikin Dakarun Najeriya, An Hallaka Yan Lakurawa
- Rundunar sojin Nijar ta tabbatar da kashe mayakan Lakurawan da su ka kutsa kasar a samame da suka kai a yankin Illela na jihar Tahoua
- An samu rahoton cewa sojojin Najeriya sun fatattaki Lakurawan, inda su ka tsallaka cikin Nijar bayan sun kasa jure harin dakarun kasar nan
- Sojojin Nijar da Najeriya su na aikin jadin gwiwa domin dakile yunkurin ƴan ta'addan da kowace kasa ke fatattaka domin kawo karshensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jamhuriyar Nijar - Rundunar sojin Nijar ta bayar da tabbacin cewa dakarunta sun hallaka wasu daga cikin 'yan ta’addan Lakurawa.
Rundunar ta bayyana cewa Lakurawan sun kutsa jamhuriyyar ne ta Kudu maso Yammacin Nijar domin cigaba da miyagun ayyukansu.
BBC Hausa ta ruwaito cewa rundunar sojin Nijar ta ce an samu nasarar ne a ranar 21 Nuwamba bayan zaratan dakaraunta sun kaddamarwa Lakurawan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lakurawa sun kashe bayin Allah a Nijar
Rahoton sojin Nijar ya tabbatar da cewa Lakurawan da su ka shiga kasar daga Najeriya sun kashe wasu daga cikin mazauna jamhuriyyar.
Rahoton ya ce;
"Yan ta'adda ne da ake kira Lukurawa sun ɓulla a jihohi Arewa maso Yammacin Najeriya musamman, Kebbi da Sokoto da suke da iyaka da jihohin Jamhuriyar Nijar wato Dosso da Tahoua, inda su ka kashe mutum 15."
Yadda aka hallaka Lakurawa a kasar Nijar
A cewar rahoton rundunar sojin Nijar, an kashe yan ta’addan Lakurawa a lokacin da jami'an tsaro suka kai samame a garin Muntseka, yankin Illela, wanda yake kusa da kan iyakar jihar Tahoua.
A cewar rahoton;
"Wataƙila sun gudu ne daga Najeriya suka shiga Nijar domin tserewa daga fatattakar da sojojin Najeriya ke musu.”
“An kori Lakurawa daga Najeriya,” Sanata
A wani labarin kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun fatattaki yan ta’addan Lakurawa da suka ya da zango a sassan jiharsa.
Ya bayar da tabbacin cewa sun samu rahoton babu sauran Lakurawa a Kebbi, domin an fatattake su bayan samun karin kayan aiki da sojoji suka yi, kuma an sun tsere zuwa jamhuriyyar Nijar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng