Trump Ya Yiwa Najeriya Barazana kan Ci Gaba da Tsare Kasurgumin Dan Ta'addan IPOB?
An samu bullar wani bidiyo da ke nuna zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana neman gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A cikin bidiyon, an ji Trump na ba gwamnatin Najeriya wa'adin 31 ga Nuwamba ta saki kasurgumin dan ta'addan kungiyar IPOB ko ta fuskanci fushinsa.
Trump ya yi barazanar janye tallafin kiwon lafiya, kudi da na jin kai daga Najeriya a cikin faifan bidiyon da aka wallafa a TikTok.
Ya kuma yi gargadin cewa Najeriya za ta fuskanci takunkumi idan kasar ba ta bi bukatarsa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya umarci Najeriya ta saki Kanu
A cikin bidiyon, an ji Trump yana cewa:
"Ina kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta sakin Mista Nnamdi Kanu, wanda ake tsare da shi a cikin yanayi mai kama da rashin adalci da tauye 'yancin ɗan adam."
“Ci gaba da tsare Nnamdi Kanu da gwamnatin Najeriya ke yi ya saba da tsarin mutunta ka’idojin ‘yanci da bin doka da oda.
“Idan ba a saki Mista Kanu ba kafin ranar 31 ga Nuwamba, 2024, gwamnatina za ta fara shirin janye tallafin jinya, kudi da na jin kai da muke baiwa Najeriya.
"Bugu da kari, idan Najeriya ta ki sakinsa, zan gana da sauran shugabannin duniya mu tattauna a kai tare da daukar mataki a kan Najeriya."
An raba bidiyon a ranar 16 ga Nuwamba ta shafin @QueenOfAll akan dandalin TikTok.
Mutane sama da 339,000 ne suka kalli bidiyon, sama da 886 suka raba shi yayin da mutane 703 suka yi sharhi a kansa.
Nnamdi Kanu dai yana hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan da aka dawo da shi daga kasar Kenya a watan Yunin 2021 inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.
An yi bincike kan bidiyon Trump
TheCable ta gano cewa faifan bidiyon da aka yi amfani da shi a cikin bidiyon na TikTok an tsakuro shi ne daga daga jawabin nasarar Trump ne.
Trump ya yi jawabin ne jim kadan bayan ya lashe zaben Amurka a ranar 6 ga Nuwambar 2024.
Wa'adin da ake zargin Trump ya sanya na ranar 31 ga Nuwamba ya sanya ayar tambaya kan sahihancin bidiyon domin Nuwamba na da kwanaki 30 ne kawai.
An kuma lura da kyaftawar idanuwan Trump da rashin daidaito tsakanin motsin labbansa da muryarsa wadanda suka kara zama ayar tambaya kan sahihancin bidiyon.
Bidiyon Trump: Gaskiya ne ko karya?
Maganar cewa Trump ya baiwa gwamnatin Najeriya wa'adin ranar 31 ga watan Nuwamba ta saki Nmamdi Kanu karya ce.
Shi kansa bidiyon da aka wallafa a matsayin jawabin Trump din na bogi ne, an yi amfani da fasahar AI wajen hada sa.
Kalli bidiyon a kasa:
Okorocha na so Tinubu ya saki Kanu
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya roki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta saki Nnamdi Kanu.
Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya tsoma baki a cikin lamarin, domin ganin Kanu ya shaki 'yanci.
Asali: Legit.ng