Hana Jagoran Lakurawa Aure Ya Jawo Arangama, Rayuka Sun Salwanta a Nijar
- Wani sabani ya jawo matsala yayin da wasu mayakan kungiyar Lakurawa su ka kashe mazauna jamhuriyyar Nijar
- Mutane akalla biyar ne su ka riga mu gidan gaskiya bayan Lakurawa sun dirar masu saboda an hana su aure
- Lamarin ya afku a garin Gueza da ke Dosso a jamhuriyyar Nijar inda daya daga cikin shugabannin Lakurawa ya je neman aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jamhuriyar Nijar - Mayakan kungiyar ta'addanci ta Lakurawa sun tafka tsiya a Gueza dake Dosso a jamhuriyar Nijar.
Mutane biyar miyagun yan ta'addan su kashe a jerin hare-hare guda biyu da su ka kai garin domin nuna bacin ransu kan hana su aure.
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa Lakurawan sun yi kisan rashin imani a kauyen, wanda ya jefa jama'a a cikin dar-dar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lakurawa sun fara kashe bayin Allah
Jaridar The Cable ta wallafa cewa yan ta'addan Lakurawa sun fara kashe jama'a saboda sun gaza samun abin da su ke so.
A baya bayan nan ne su ka kaddamar da mugun hari a garin Gueza bayan an hana jagoransu auren yar garin, lamarin da ya jawo fargaba.
Yadda Lakurawa su ka far wa Nijar
Rahotanni sun bayyana cewa daya daga jigon Lakurawa ne ya nuna kaunarsa ga wata mata a kauyen, lamarin da mai unguwa ya nuna rashin din dadinsa.
Wannan ta sa iyayen matar su ka tura ta wajen wasu yan uwansu a wajen gari, hakan kuma ya fusata Lakurawan matuka.
A zuwan farko, an ruwaito miyagun mutanen sun shaƙe mutane biyar har sai da su ka daina motsi, a zuwa na biyu kuma sun kashe wakilin mai gari.
Ana shirin maganin Lakurawa
A baya mun ruwaito cewa Najeriya ta tabbatar da shirinta na fatattakar Lakurawa da su ka ya da zango a wasu daga cikin jihohin kasar da ke Arewa maso Yamma a cikin gaggawa.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayar da tabbacin yayin ziyarar aiki da duba wasu jiragen yaki da aka kawo Najeriya domin karfafa yaki da ta'addanci a Arewa.
Asali: Legit.ng