Hattara Yan TikTok: An Daure Matashi a Gidan Kaso kan Zagin Shugaban Kasa

Hattara Yan TikTok: An Daure Matashi a Gidan Kaso kan Zagin Shugaban Kasa

  • Wani matashi dan TikTok a kasar Uganda ya gamu da matsala bayan yanke masa hukuncin daurin watanni 32 a gidan kaso
  • Kotu a kasar Uganda ta daure matashin mai suna Emmanuel Nabugodi kan zagin Shugaba Yoweri Museveni a manhajar TikTok
  • Hakan ya biyo bayan amsa dukan laifuffukan da ake zargin Nabugodi ya aikata da suka hada da taba kimar shugaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kamfala, Uganda - Wata kotu a kasar Uganda ta daure matashi dan TikTok mai shekaru 21 a gidan gyaran hali kan taba kimar shugaban kasa.

Kotun ta daure matashin, Emmanuel Nabugodi watanni 32 a gidan kaso bayan fitar da wani faifan bidiyo a TikTok da aka zargi yana zargin shugaba Yoweri Museveni.

An daure dan TikTok kan zagin shugaban kasa
Kotu a Uganda ta daure matashi a gidan kaso kan cin mutuncin shugaban kasa. Hoto: Apex FM Tv.
Asali: Youtube

Kotu ta daure matashin dan TikTok a Uganda

Kara karanta wannan

Haraji: Bayan barazanar gwamnoni, majalisa ta yi magana kan buƙatar Tinubu

An yankewa Nabugodi hukuncin ne a jiya Litinin 18 ga watan Nuwambar 2024 bayan ya amince da aikata laifuffuka hudu da ake zarginsa a kai a cewar BBC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin laifuffukan da ake zargin Nabugodi akwai yada kalaman kiyayya ga shugaban kasar da suka saba doka.

A cikin bidiyon da ya yi kan wata shari'ar izgili da ake yiwa Museveni, Nabugodi ya yi kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama'a.

Yayin hukuncin, Mai Shari'a, Stellah Maris Amabilis ta ce Nabugodi bai yi nadamar abin da ya aikata ba.

Amabilis ta ce hakan zai zama izina ga wasu a kafofin sadarwa kan yadda ake cin mutuncin jama'a ciki har da taba kimar shugaban kasa.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi ta kiran a saki matashin inda suka koka kan rashin ba al'umma damar fadan albarkacin bakinsu.

An tura dan TikTok gidan kaso a Uganda

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bukaci Tinubu ya kori shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya ba da dalili

Kun ji cewa Kotu ta yankewa wani ɗan Uganda, Edward Awebwa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari bisa zargin zagin shugaba Yoweri Museveni da iyalansa a TikTok.

Edward Awebwa mai shekara 24 a duniya ya amsa laifin yin kalaman ƙiyayya da yada labaran ƙarya, amma bai nuna nadama a gaban kotu ba.

Hukuncin dai ya janyo damuwa daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama, waɗanda ke zargin cewa ya keta ƴancin faɗin albarkacin baki, kuma wani yunƙuri ne na murkushe masu caccakar gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.