Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa

Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa

A kokarinsa na son bunkasa diya ta hanyar aikin gona, shugaban kasar Uganda ya yanke shawarar nunawa mutane yadda zasu bi game da dukkan aiki, da kansa.

Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa
Shugaban kasar Uganda dauke da ruwa zuwa gonarsa

Shugaban kasa Yoweri Kguta Museveni  na kasar Uganda, ya yanke shawarar nuna yadda ya dauki bunkasa arzikinsa da muhimmanci.

An nuno  Museveni  yana diban ruwa a kan kekensa, yayinda ya mika zuwa gonan gwamnati don yin banruwa ga shukokin da ya rigada ya shuka.

Da ya yada rubutun a kan shafinsa na Facebook, Museveni ya rubuta:

Yau ne rana na uku na shirin bunkasa dukiyata da nake yi a Luweero. A safiyar nan, Na dubo ruwa a kan kekena don nuna yadda ake shuka Coffee da ayaba da na shuka a gonan gwamnati dake kauyen Kawumu,yankin  Luweero. Zanci gaba da daki-daki nan a janyo hankulan jama’a da kuma wayar masu da kai a kan aikin samar da dukiya.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kebbi da tawagarsa sun ziyarci gonan shinkafa

Ga hotunan a kasa:

Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa
Shugaban kasar Uganda Museveni lokacin da yake diban ruwa zuwa gonarsa
Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa
Shugaban kasa Museveni a hanyarsa ta zuwa gona don baruwa
Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa
Shugaban kasar Uganda na tone kasa don yin shuka
Anga shugaban kasar Uganda yana diban ruwa zuwa gonarsa
Shugaban kasar Uganda

Babu shakka hakan zai karfafa wa jama'a gwiwa!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng