Tinubu Ya Fadi Dalilin Najeriya na Shiga Sabuwar Kungiyar Kawancen Kasashen Duniya

Tinubu Ya Fadi Dalilin Najeriya na Shiga Sabuwar Kungiyar Kawancen Kasashen Duniya

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya Najeriya cikin sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya da aka kafa a Brazil
  • Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya kirkiro kungiyar da nufin yakar yunwa da talauci a kasashen duniya
  • A yayin taron G20, Tinubu ya ce amincewar Najeriya da kafuwar kungiyar zai cimma burinta na kawar da yunwa da fatara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Brazil - Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa kungiyar kawancen kasashe kan yaki da yunwa da talauci wadda shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya gabatar.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wajen bude taron shugabannin kungiyar G20 karo na 19 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.

Tinubu ya yi magana kan dalilin shigar Najeriya cikin kungiyar kawancen kasashen duniya
Tinubu ya amince da kafa kungiyar kawancen kasashen duniya kan yaki da yunwa, talauci. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A yayin taron, shugaba Tinubu ya bayyana irin wannan kawancen a matsayin wani babban jigon yaki da yunwa da fatara a duniya, inji rahoton Channels.

Kara karanta wannan

Abu ya faskara: Dangote na neman bashin biliyoyin daloli domin shigo da danyen mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya amince da kungiyar kawance

Tinubu ya yaba da shirin kawancen tare da bayyana shi a matsayin matakin da ya dace domin magance daya daga cikin manyan kalubalen duniya.

"Wannan babban mataki na hangen nesa yana nuna fifikon Brazil wajen magance daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar duniyarmu a yau.
"Ƙirƙirar wannan kungiya ya zama gagarumin ci gaba a ƙoƙarinmu na kawar da yunwa da fatara, kuma sako ne na haɗin kai ga kasashe masu rauni a duniya."

- A cewar Tinubu.

Amfanin kungiyar ga ci gaban Najeriya

Tinubu ya ce irin wannan hadakar na daga cikin abubuwa takwas da ya yi magana kansu a jawabin rantsar da shi watanni 18 baya, wanda ya ce zai taimaki tattalin arzikin kasar.

A cewar shugaba Tinubu, amincewar Najeriya na shiga wannan kungiyar wani mataki ne na kasar a yakin da take yi na kawar da yunwa da talauci, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Lalacewar wuta, tsadar fetur da matsalolin da suka jefa talaka a mawuyacin hali

Ya kara da cewa, ta hanyar nuna goyon baya ga shirin hadakar, Najeriya ta nuna kokarinta na cimma muradun karninta, musamman bangaren yaki da fatara, da samar da abinci.

Tinubu ya isa taron G20 a kasar Brazil

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya shilla zuwa kasar Brazil domin halartar taron shugabannin kasashen G20.

A gefen taron, ana sa ran shugaba Tinubu zai gudanar da zama domin ci gaba da tallata manufar sake fasalin tattalin arziƙin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.