Tarihi da Muhimman Abubuwa kan Taron Kasashen Musulmi da Tinubu ya Halarta
- A makon da muke ciki aka gabatar da taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi a Saudiyya
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na cikin shugabannin duniya da suka halarci taron a birnin Riyadh na kasar Saudiyya
- A wannan rahoton, mun tattaro muku tarihi da wasu muhimman abubuwa kan taron kasashen Musulmi da ake yi duk shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da kasashen Musulmi sun yi taro na musamman kan yakin da ake yi a Gaza da Lebanon.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sha suka kan halartar taron kasashen Musulmi daga wasu yan Najeriya.
A wannan rahoton, mun tattaro muku muhimman abubuwan kan yadda aka fara taron kasashen Musulmi na duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen da ke zuwa taron Musulmi
Dukkan kasashen Larabawa na cikin mambobin da suka halartar taron kasashen Musulmi na duniya.
Sai kuma sauran ƙasashen da ba na Larabawa ba amma suna karkashin kungiyar kasashen Musulmi ta (OIC) wanda a dalilin haka ne Najeriya ke halartar taron.
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa Kungiyar OIC ta haɗa kasashen Larabawa da sauran ƙasashen da ba na Larabawa ba amma Musulmi ne mafi rinjaye ko suna da yawa.
Yaushe aka kafa kungiyar OIC a duniya?
A shekarar 1969 kasashen Musulmi 24 suka taru a kasar Morocco domin fara magana kan kafa kungiyar OIC.
Taron da suka yi a Morocco ya biyo bayan wani hari ne da aka kai Masallacin Kudus wanda ya lalata wani bangare na rufin masallacin.
Daga nan kuma kungiyar ta sake wani taro a shekarar 1970 a kasar Saudiyya inda ta bude sakatariya a kasar.
Manufar kafa kungiyar OIC a 1969
An kafa kungiyar OIC ne domin kare daraja da mutuncin dukkan kasashen Musulmi a fadin duniya.
A karkashin haka ne ma kungiyar ta shirya taron shekarar 2024 domin samar da mafita a kan yaki da ake a Gaza da Lebanon.
Kasashe nawa ne a ƙungiyar OIC?
Duk da cewa kungiyar OIC ta fara da kasashe 24, a yanzu haka tana da mambobi a kasashen duniya har guda 57.
OIC ce kungiyar kasashe mafi girma a duniya bayan majalisar dinkin duniya da ta haɗa mafi yawan kasashen duniya.
Yaushe Najeriya ta shiga OIC?
Tun farar safiya da aka kafa kungiyar OIC Najeriya ke cikin tafiyar duk da cewa ba ta zamo cikakkiyar yar kungiyar ba.
The Nation ta wallafa cewa bayan shekaru 17 da zama mamba ta wucin gadi a ƙungiyar, Najeriya ta zamo cikakkiyar yar OIC a shekarar 1986.
A karon farko, Janar Yakubu Gowon ne ya jagoranci saka Najeriya a kungiyar OIC a lokacin da kasar ke fama da yakin basasa.
Taron kasashen Musulmi na 2024
Taron kasashen Musulmi da aka yi a shekarar 2024 ya haɗa kungiyoyin OIC da sauran ƙasashen Larabawa.
Kuma kasashen sun tattauna ne a kan yadda za a samu maslaha kan rikicin Falasɗinu da Isra'ila da kuma rikicin Lebanon.
Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta wallafa cewa dukkan kasashen Larabawa da kungiyar OIC sun bukaci a kawo karshen zubar da jini a Gaza.
Matsayin Najeriya kan rikicin Gaza
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci a samar da halastacciyar kasar Falasɗinu a yankin Gaza.
Bola Ahmed Tinubu ya wallafa a Facebook cewa samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta za ta taimaka wajen kawo karshen yakin da ake a Gaza.
Gwamnatin Najeriya ta ce bai kamata a bar rikicin ya cigaba ba kasancewar ana keta hakkin dan Adam a cikinsa.
Kasar Saudiyya za ta tallafi Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ranar Litinin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Muhammad bin Salman.
A yayin wata tattaunawa da suka yi, gwamnatin Saudiyya ta yi alkawarin cigaba da tallafawa tattalin Najeriya musamman a harkar noma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng