Tun Kafin Shiga White House, Trump Ya Fara Maganar Wa'adin Mulki Karo na 3 a Amurka

Tun Kafin Shiga White House, Trump Ya Fara Maganar Wa'adin Mulki Karo na 3 a Amurka

  • Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya fara maganar yiwuwar cigaba da mulki karo na uku tun kafin a rantsar da shi
  • Donald Trump zai fara wa'adi na biyu ne bayan kayar da Kamala Harris a zaben Amurka da ya gudana a makon da ya wuce
  • Haka zalika Trump ya zanta da shugaba Joe Biden inda ake sa ran za su tattauna kan yadda za a mika masa mulki a 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington D.C, America - Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya fara maganar zarcewa a kan mulki.

A dokar Amurka, sau biyu za a rantsar da shugaba kuma a shekara mai zuwa Trump zai yi rantsuwa karo na biyu.

Trump
Trump ya fara maganar tazarce. Hoto: Donald J. Trump
Asali: Getty Images

Gulf News ta wallafa cewa Donald Trump zai gana da Joe Biden a fadar White House a yau Laraba.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya mai kuɗi ya kashewa budurwa Naira miliyan 800 a tashi daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Donald Trump ya fara maganar tazarce

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya fara zancen tazarce bayan samun nasara a zaben Nuwamba.

Yunkurin tazarce zai zamo ya saba dokar Amurka kasancewar Donald Trump ya ci zaben shugaban kasa har sau biyu.

"Ba na tunanin tazarce sai dai idan magoya baya na sun ce na cancanci hakan."

- Donald Trump

Maganar tazarcen da zababben shugaban kasar ya yi ta sanya magoya bayansa tintsirewa da dariya

Trump ya gana da Joe Biden

New York Times ta wallafa cewa a yau Laraba ne Donald Trump ya gana da shugaban kasar Amurka, Joe Biden a fadar White House.

Ana sa ran cewa shugabannin sun tattauna ne kan yadda za a mika mulki ga Donald Trump a shekara mai zuwa.

Masana na ganin cewa Joe Biden ya girmama Donald Trump bisa gayyatar kasancewar bai yi wa Biden haka ba yayin da ya ci zaɓe a 2020.

Kara karanta wannan

Ana masa dawo dawo karo na 2, Jonathan ya yi magana kan nasarar Trump

Trump ya ba Elon Musk mukami

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya sakawa abokinsa, Elon Musk da babban mukami a gwamnati.

An ruwaito cewa Donald Trump ya amince da nadin Musk da Vivkek Ramaswamy domin jagorantar hukumar inganta ayyukan gwamnati (DOGE).

Muhammad Malumfashi babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng