Bayan Ɓullar Lakurawa, Kwamandan Sojin Amurka Ya Zo Najeriya
- Kwamandan sojojin Amurka mai kula da yankin Afrika, Janar Micheal Langley ya kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro
- An ruwaito cewa Janar Michael Langley ya gana da babban hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa a birnin tarayya Abuja
- Ziyarar Janar Micheal Langley ta kasance ne a lokacin da dakarun sojin Najeriya ke yaki da yan ta'addar Lakurawa da suka ɓulla a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da cewa kwamandan sojojin Amurka mai kula da Afrika ya ziyarci Najeriya.
Janar Micheal Langley ya kawo ziyara Najeriya ne domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da yadda za a magance su.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Janar Michael Langley ya gana da hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban sojan Amurka ya zo Najeriya
Kwamandan sojin Amurka mai kula da Afrika ya gana da hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
Rundunar tsaron ta tabbatar da cewa Janar Michael Langley ya samu rakiyar Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills.
Menene ya kawo sojan Amurka Najeriya?
Janar Micheal Langley ya zo Najeriya domin tattaunawa kan yadda za a cigaba da yaki da yan ta'adda a yankunan Afrika.
The Nation ta wallafa cewa Janar Michael Langley ya yabawa Najeriya kan salon da take bi wajen yaki da yan ta'adda.
Rundunar tsaron Najeriya ta ce za ta cigaba da yakar yan ta'adda kuma ta bukaci taimakon Amurka.
"Janar Musa ya bukaci hadin kan kasar Amurka musamman wajen ba sojoji horo da sayen makamai.
Ya kuma mika godiya ga Janar Micheal Langley bisa kokarin da ya yi na ziyartar rundunar tsaron Najeriya."
- Birgadiya Janar Tukur Gusau, jami'in yada labaran rundunar tsaro
An saka ranar birne hafsun sojoji
A wani rahoton, kun ji cewa an saka ranar jana'izar tsohon shugaban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, marigayi Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.
Babban yayan marigayin ya bayyana cewa za a birne Laftanar Janar Lagbaja a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng