Bayan Gagarumar Gudunmawa a Zaben Amurka, Trump Ya ba Elon Musk Muƙami
- Shugaban kasar Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya sakawa abokinsa, Elon Musk da babban mukami a gwamnati
- Trump ya amince da nadin Musk da kuma Vivkek Ramaswamy domin jagorantar hukumar inganta ayyukan gwamnati (DOGE)
- Hakan bai rasa nasaba da irin gudunmawa da suka ba shi musamman shi shugaban kamfanin Tesla da X yayin kamfe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Washington DC, Amurka - Sabon shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya fara yin nade-nade a gwamnatinsa.
Donald Trump ya nada Elon Musk a matsayin wanda zai jagoranci hukumar kula da ingancin gwamanti (DOGE) a Amurka.
Donald Trump ya ba Elon Musk muƙami
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a jiya Talata 12 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya nada Musk ne da Vivkek Ramaswamy domin jagorantar hukumar saboda kawo sauyi da kuma sauya tsarin hukumomin kasar.
Sabon shugaban ya nada mutanen biyu domin kawo sauyi kan yadda ake gudanar da mulki a kasar da kuma rage yawan jinkiri a gudanar da harkokin gwamnati.
Abin da ake tsammani daga Musk, Ramaswamy
Za su tabbatar da rage yawan ka'idoji da ke kawo tarnaki a harkokin gwamnati da rage yawan kashe kudi.
"Ina mai farin cikin sanar da nada Elon Musk da Vivkek Ramaswamy mukami domin jagorantar hukumar 'DOGE' a Amurka."
"Tare da aiki da wadannan jajirtattu, za mu rage yawan kashe kudi a gwamnati da kaso sauyi a hukumomin kasar."
"Hakan zai rage yawan kashe-kashen kudi da kuma tarnaki da ake samu kan ayyukan gwamnati."
- Donald Trump
Arzikin Elon Musk bayan nasarar Donald Trump
A baya, kun ji cewa nasarar Donald Trump a Amurka ta jawowa attajirin duniya, Elon Musk riba inda dukiyarsa ta karu da $13bn cikin awanni kadan.
Musk wanda ya ke goyon bayan takarar Trump tun daga tushe ya samun ribar a hannayen jari da dama a kamfaninsa na Tesla.
Wannan na zuwa ne bayan sanar da nasarar Trump karo na biyu a zaben kasar Amurka inda ya kayar da Kamala Haris.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng