Gaskiya Ta Fito kan Saukar Dusar Ƙanƙara a Ɗakin Ka'aba

Gaskiya Ta Fito kan Saukar Dusar Ƙanƙara a Ɗakin Ka'aba

  • A safiyar yau aka samu wasu mutane a kafafen sada zumunta na yada cewa an samu saukar dusar ƙanƙara a masallacin Ka'aba
  • Biyo bayan lamarin, hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana halin da ake ciki tare da yin kira na musamman ga al'ummar Musulmi
  • Wasu mutane da suke zaune a kasar Saudi sun bayyana cewa bayanan da hukumomin kasar suka yi game da lamarin gaskiya ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta yi bayani kan wasu hotuna da aka haɗa a kafafen sada zumunta game da ɗakin Ka'aba.

Wasu mutane ne suka hada hoton dakin Ka'aba da ke nuna an samu saukar dusar ƙanƙara a masallacin Makka mai alfarma.

Saudiyya
Saudiyya ta karyata saukar dusar kankara a Ka'aba. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da shafin kasar Saudiyya, Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun zo da ta'addanci, sun yi barna a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu dusar ƙanƙara a dakin Ka'aba

Hukumomin kasar Saudiyya sun ƙaryata cewa an samu saukar dusar ƙanƙara a masallacin Haramin Makka.

Kasar Saudiyya ta ce sam babu ƙamshin gaskiya cikin labarin kuma ta yi gargadi kan hada labarai marasa tushe.

" Babu dusar ƙanƙara a Masallacin Ka'aba. Yana da muhimmanci a rika bincike daga kafofi masu inganci.
Irin waɗannan labarun za su yadu cikin kankanin lokaci kuma za su iya kawo ruɗani.
Ku rika tabbatar da gaskiyar zance daga kafofi masu tushe kafin yada su."

- Inside the Haramain

Wata mai amfani da kafar Facebook, Shamrat Hassan ta ce a yanzu haka tana kasar Saudiya amma babu alamar saukar dusar ƙanƙara.

Wani mai suna Assan a kafar Facebook ya ce yadda mutane ke yada labarun karya kuma za su iya shiga motar Dajjal cikin sauki.

An nada liman masallatan Harami

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta yi sauye sauye a masallatai masu alfarma na Makka da Madina. a ranar Alhamis

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka wani bawan Allah ana saura ƴan kwanaki ɗaurin aurensa

Rahotanni sun tabbatar da cewa an nada sababbin limaman dindindin da za su rika jagorantar salla a masallatai masu alfarma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng