Jill Stein da ‘Yan Takaran da Suka Nemi Mulkin Amurka Tare da Trump da Harris
- Tsohon shugaba Donald J. Trump ya lashe zaben Amurka da mafi rinjayen kuri’u da kuma kuri’un wakilan masu zabe
- Kamala Harris da ta samu tutar jam’iyyar Democrats mai-ci ba ta yi galaba ba, amma ta sha gaban wasu ‘yan takara
- Jill Ellen Stein da Robert Francis Kennedy Jr. su na cikin wadanda suka nemi kujerar shugaban Amurka a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
United States - Yanzu kusan babu labarin da ake yi a duniya kamar nasarar Donald J. Trump a kan Kamala Harris a zaben da ya gabata.
Baya ga ‘yan takaran jam’yyun Republican da Democrats, akwai wasu ‘yan siyasar da suka nemi mulkin, sai dai su ba su shahara sosai ba.
Sauran 'yan takaran shugaban kasa a Amurka
Rahoton nan ya kawo wasu boyayyun ‘yan takaran da suka nemi shugabancin Amurka a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Jill Stein
Jill Ellen Stein kwararriyar likita ce kuma ‘yar gwagwarmaya wanda ta nemi zama shugaban kasar Amurka a wannan zaben da aka yi.
Ita Jill Ellen Stein ta tsaya takara ne a jam’iyyar Green Party wanda ta saba yi mata takara kafin neman kujerar shugaban kasar nan da ta yi.
A zabukan 2012 da 2016, ta nemi mulki amma Barack Obama ya yi galaba a kan ta kuma ta nemi takarar gwamnar Massachusetts sau biyu.
Wani rahoton da Aljazeera ta fitar ya nuna yadda likitar ta yi tasiri a zaben shekarar nan.
Akwai masu ganin duk wanda ya zabi Jill Stein tamkar ya goyi bayan Donald Trump ne wanda dama shi ya taba nuna ta na burge shi.
Kamala Harris da jam’iyyar Democrats sun kashe kudi domin ganin mutane ba su zabi irinsu Stein ba musamman a jihohin da suke da karfi.
2. Robert Kennedy
Robert Francis Kennedy Jr. da ya fi shahara da RFK Jr fitaccen ‘dan siyasa ne a Amurka wanda ya so ya nemi takarar shugaban kasa a 2024.
Da jin labarin Donald Trump ya kai labari, Robert Francis Kennedy Jr. ya fito ya na mai taya shi murna, ya yi magana ne a shafinsa na X.
‘Dan takaran wanda salinsa lauya ne ya fito ne daga gidan Kennedy wanda duniya ta san gudumuwar da suka ba da a siyasar kasar Amurka.
Robert Francis Kennedy Jr. ya yi suna wajen yakar rigakafin annobar cutar COVID-19.
Times of India ta kawo shi cikin ‘yan takaran da aka fito neman mulki da su, daga baya ya janye ya na mai goyon bayan Donald J. Trump.
3. Chase Oliver
Shi ma Chase Russell Oliver wani ‘dan gwagwarmaya ne da ya fito neman kujarar shugaban kasa a zaben 2024, amma bai kai labari ba.
Chase Russell Oliver ya samu tikitin jam’iyyar Libertarian Party da kyar a wani zaben tsiada gwani da ya yi zafi sosai a watan Mayun 2024.
Jaridar NY Times ta rahoto cewa ‘dan takaran ya bayyana kan shi a matsayin ‘dan luwadi, ya fito neman mulkin yana mai shekara 39.
Lokacin kamfe, an jiOliver bai goyon bayan hana rike bindiga kuma ya goyi bayan a yi wa kundin tsarin mulkin Amurka garambawul.
‘Dan siyasar da ya nemi Sanata a zaben 2022 ya jawo aka yi zagaye na biyu tsakanin Raphael Warnock da Herschel Walker a Georgia.
Bai kaunar yakin da Israil ta ke yi a Gaza kuma daga cikin inda ya yi tarayya da Democrats shi ne goyon bayan zubar da ciki da shan wiwi.
Yaushe Trump zai karbi mulkin Amurka?
Duk da cewa Donald Trump ya lashe zabe, ba yanzu zai shiga White House ba kamar yadda aka yi wani bayani a wani rahoto da aka fitar.
Ana rantsar da zababben shugaban kasa watanni bayan kammala zaben. Za a rantsar da Trump da a cikin watan Janairun shekarar 2025.
Asali: Legit.ng