Trump Ya Fara Aiki a Matsayin Zababben Shugaban Amurka Tun Kafin Ya Shiga Ofis
- Zababben shugaban Amurka, Donald Trump ya fara shirin tafiyar da harkokin kasar duk da akwai sauran lokaci kafin ya shiga ofis
- Daga cikin manya manyan abubuwan da Trump ya yi akwai nadin wanda za ta zama shugabar ma'aikatan fadar 'White House'
- Donald J Trump ya kuma bayyana aniyarsa ta tattaunawa da Rasha domin dakatar da yaki da Ukraine da aka shafe lokaci ana yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Amurka - Zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi nadin farko a gwamnatin da za ta karbi ta Joe Biden nan da wasu watanni masu zuwa.
Trump ya nada Susie Wiles a matsayin shugabar ma'aikatan fadarsa ta White House, ita ce mace ta farko da ta rike mukamin a tarihin Amurka.
BBC ta wallafa cewa Donald Trump ya yabi Susie Wiles bisa muhimmiyar rawa da gwagwarmayarta a dawowarsa a matsayin zababben shugaban kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump ya fara nadi a gwamnatinsa
Susie Wiles ta taka rawar gani a matsayin shugabar yakin neman zaben Donald Trump a zaben 2024 inda ya zama zababben shugaban Amurka karo na 47.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa haka shi kuma Trump ya fara kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine inda ya ce zai tattauna da Vladimir Putin.
Trump na shirin shawo kan yakin Rasha - Ukraine
Zababben shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya na fatan tattaunawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, duk da ya ce sun jima ba su gana ba.
Trump ya bayyana fatan kyakkyawar alakarsa da Putin za ta taimaka ainun wajen cimma matsaya kan yakin Rasha da Ukraine da aka fara a 2022.
Trump ya yi nasara a zaben Amurka
A baya kun ji cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald J Trump ya yi nasara a zaben shugaban kasar bayan fafatawa da mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Haris.
Zaben da aka yi a ranar Talata ya kafa tarihi a siyasar Amurka, inda Trump ya zama shugaban kasa da aka zaba sau biyu a lokuta mabanbanta domin jagorancin jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng