Dan Najeriya Ya Yi Damfarar Miliyoyin Daloli a Amurka, Kotu Ta Daure Shi
- Wani dan asalin Najeriya mai rike da shaidar dan kasa ta Burtaniya ya debo ruwan dafa kansa bayan tafka damfara
- An kama wani Oludayo Adeagbo da wasu mutane da zargin damfarar mutane daban daban a Amurka Dala miliyan biyar
- Kotu ta yanke masu hukuncin biyan tarar Daloli da kuma shekaru bakwai a gidan kurkurun kasar domin ya girbi abin da ya shuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar America - Wani dan asalin Najeriya mai shaidar dan kasar Burtaniya, Oludayo Adeagbo ya jefa kansa a cikin gagarumar matsala.
A cewar ma’aikatar shari’ar kasar Amurka, Adeagbo, wanda ke amsa sunan John Edwards da John Dayo ya hada baki da wasu wajen tafka damfarar miliyoyin Dala.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Oludayo Adeagbo ya damfari hukumomin Texas, ciki har da kananan hukumomi, kamfanonin gine-gine da wata kwalejin yankin Houston.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka: An kama dan Najeriya saboda damfara
Arise Television ta tattaro cewa an kama dan asalin Najeriya, Oludayo Adeagbo da wasu mutane biyu da laifin damfarar $5m a wurare daban daban a Amurka.
An gano yadda Adeagbo ya hada baki da wasu wajen damfarar jami'ar Carolina tsabar kudi $1.9m, kuma tuni wadanda ake tuhuma su ka amsa laifinsu.
Kotu ta yanke hukunci kan damfara a Amurka
A ranar A ranar 8 ga Afrilu, Adeagbo ya amsa tuhume tuhume guda biyu da aka yi masa a North Carolina da Texas da Carolina inda ya tafka zambar.
Kotu a kasar ta Amurka ta umurci Adeagbo da ya biya diyyar $942,655.03, sannan an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai.
Najeriya ta mayar da kudin Damfara Amurka
A baya mun wallafa cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta mayar da wasu makudan kudade Amurka da wani dan Najeriya ya yi damfarar su.
Hukumar EFCC ta bakin jami'in huldarta, Dele Oyewale ya bayyana cewa za su cigaba da aikin hana yin zagon kasa a Najeriya bayan an cafke wani Hakeem da gurfanar da shi kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng