Donald Trump: Yaushe Zababben Shugaban Kasar Amurka Zai Shiga Fadar White House?

Donald Trump: Yaushe Zababben Shugaban Kasar Amurka Zai Shiga Fadar White House?

  • Tsohon shugaban kasa, Donald Trump ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talata, 5 ga Nuwambar 2024
  • Duk da cewa a ranar 6 ga Nuwamba aka tabbatar da nasarar Trump, sai dai ba zai shiga ofis ba har sai bayan wasu watanni da zaben
  • Kundin tsarin mulkin kasar, ya kayyade cewa za a rantsar da zababben shugaban kasa da mataimakinsa a ranar 20 ga Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - A ranar Laraba ne aka sake zabar Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka kuma nan ba da jimawa ba zai koma fadar White House.

Donald Trump ya samu nasara kan mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris shekaru hudu bayan shan kaye a neman tazarcensa a zaben 2020.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fitar da sabon kuduri da zai yi wa kujerar shugaban kasa barazana

Rahoto ya bayyana lokacin da za a rantsar da zababben shugaban Amurka, Trump
Bayan lashe zaben Amurka, an bayyana ranar da za a rantsar da Donald Trump. Hoto: @realDonaldTrump
Asali: Twitter

Duk da cewa an bayyana Trump a matsayin wanda ya yi nasara zaben, jaridar CNS News ta rahoto cewa za a shafe watanni da dama kafin Trump ya shiga ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a rantsar da Trump?

Ya zuwa ranar Laraba, Donald Trump ya samu kuri'un wakilai 277, kuma dan takara na bukatar kuri'u 270 ne domin lashe zaben shugaban kasa.

Zababben shugaba kasa Trump zai shiga ofis ne bayan an yi bikin rantsar da shi a shekarar 2025 a cewar rahoton jaridar USA Today.

A kodayaushe, kasar Amurka na gudanar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa ne a ranar 20 ga watan Janairu, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Kamar yadda binciken Legit Hausa ya nuna, 20 ga watan Janairun 2025 za ta kama ranar Litinin.

Amurka: Me ke faruwa a ranar rantsuwar?

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Kamala Harris ta kira zaɓabɓen shugaban Amurka, Trump ta wayar tarho

Zababben shugaban ya na zama shugaban kasa da zarar an rantsar da shi. Sabon shugaban ya kan koma fadar White House bayan bikin rantsuwar.

Abubuwan da ake gudanarwa a ranar bikin rantsuwar wanda ake yi a birnin Washington D.C sun hada da rantsuwar kama aiki daga bakin shugaban kasa da mataimakinsa.

Mataimakin shugaban kasar ne yake fara karanto rantsuwar kama aiki. Zuwa lokacin da rana ta take ne shugaban kasa ke karanta rantsuwar kama aikinsa.

Sauran bukukuwan sun hada da jawabin kama aiki daga bakin zababben shugaban kasar, jawabai daga manyan kasa, raye raye da kuma wake wake.

Trump ya lashe zaben Amurka

Tun da fari, mun ruwaito cewa Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar ranar Talata, 5 ga Nuwamba, inda ya doke Kamala Harris.

Wannan nasara da ya samu a zaben shugaban ya sa Trump ya shiga tarihin siyasar Amurka na sake shiga fadar White House karo na biyu a lokuta daban daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.