Joe Biden Ya Bukaci Dangote Ya Dawo da Litar Man Fetur N150?

Joe Biden Ya Bukaci Dangote Ya Dawo da Litar Man Fetur N150?

  • A makon da ya wuce aka rika yada wani bidiyo da aka ce shugaban kasar Amurka, Joe Biden ne ke ba Aliko Dangote umarni
  • A cikin bidiyon, an umarci Aliko Dangote ya dawo sayar da litar fetur a kan N150 saboda wahalar rayuwa da yan Najeriya ke fama da ita
  • Lamarin ya tilasta masana yin bincike domin gano gaskiyar maganganun da aka ce shugaba Joe Biden ya fadawa Aliko Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An gudanar da bincike kan sahihancin wani bidiyo da aka nuna shugaban Amurka, Joe Biden yana kira ga Aliko Dangote ya rage farashin man fetur.

A cikin bidiyon, mutumin da aka nuna a matsayin Joe Biden ya yi kira ga Bola Tinubu kan daidaita lamura a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ban sani ba sai daga baya," Gwamna Abba ya faɗi abin da ya faru da yaran Kano

Dangote Joe Biden
An fito da gaskiyar bidiyon da Biden ya yi magana ga Dangote kan farashin fetur. Hoto: Joe Biden|Dangote Industries
Asali: Facebook

A ranar 1 ga watan Nuwamba mai rajin kare hakkin dan Adam da aka fi sani da Very Dark Man ya wallafa bidiyon a shafinsa na TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da aka 'fadawa' Dangote a bidiyon Biden

An nuna wani mutum a matsayin Joe Biden yana kira ga Aliko Dangote ya rage kudin mai.

Ga abin da yake cikin bidiyon.

"Aliko Dangote ya kamata ka rage kudin man fetur, ka daina tsada. Ka riga ka mallaki matatar mai saboda haka ya kamata ka sayar da litar mai a N150.
Shugabannin Najeriya ba su damu da yan kasar ba, ba su tausayin talakawa. Sata kawai suka iya."

Menene gaskiya bidiyon Joe Biden?

Jaridar the Cable ta yi bincike mai zurfi kan bidiyon kuma ta gano cewa kashi 97% na shi ba gaskiya ba ne.

A karkashin haka aka gano cewa kiran da Joe Biden ya yi wa Aliko Dangote na rage kudin litar mai zuwa N150 ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya babban rashi

Da me aka hada bidiyon Joe Biden?

Bincike ya nuna cewa an hada bidiyon ne da fasahar Deepfake da ake iya kwaikwayon muryar mutane.

Saboda haka farashin litar man fetur za ta cigaba da zama a yadda take a Najeriya ba tare da samun wani sauki ba.

'Yan kasuwa sun kai Aliko Dangote kotu

A wani rahoton, kun ji cewa wasu manyan yan kasuwa a harkar man fetur sun mayar da martani kan korafin attajirin Afrika, Aliko Dangote.

Kamfanonin AYM Shafa da A. A Rano da Matrix sun bukaci kotu ta dakatar da Alhaji Aliko Dangote daga mamaye kasuwar mai a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng