Engonga: Gwamnati Ta Dauki Mataki kan Jami'in da Aka Kama Ya Yi Lalata da Mata 400

Engonga: Gwamnati Ta Dauki Mataki kan Jami'in da Aka Kama Ya Yi Lalata da Mata 400

  • Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta yanke hukunci mai tsauri kan shugaban hukumar ANIF, Baltasar Ebang Engonga
  • Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa gwamnatin kasar ta cafke Engonga bayan bullar bidiyo daban daban yana lalata da mata
  • Bayan binciken da gwamnatin ta gudanar, an kori Baltasar Engonga daga aiki, aka ce bai cancanci rike mukamin gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Equatorial Guinea - Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta kori babban daraktan hukumar binciken kudi ta kasa ANIF, Baltasar Ebang Engonga.

An kori Baltasar Engonga ne bayan da aka gano faifan bidiyo kusan 400 da ke nuna lalatar da ya yi da wasu manyan mata a kasar Equatorial Guinea.

Kara karanta wannan

"Ban sani ba sai daga baya," Gwamna Abba ya faɗi abin da ya faru da yaran Kano

Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta dauki mataki kan jami'in da ya yi lalata da mata 400
Gwamnatin Equatorial Guinea ta kori jami'inta da ya yi lalata da mata 400. Hoto: @kabumba_justin
Asali: Twitter

An kori jami'in gwamnati saboda bidiyon lalata

Jaridar Real Equatorial Guinea ta ruwaito cewa shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya ba da umarnin korar Engonga bayan bayyana bidiyon lalatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kori Baltasar Engonga Alú, wanda aka fi sani da "Bello", daga mukaminsa na shugaban hukumar binciken kudi ta Equatorial Guinea (ANIF) a cewar rahoton.

Da take ambaton doka mai lamba 118/2024, mai kwanan wata 4 ga watan Nuwamba, jaridar ta ce an kori Engonga ne bisa zargin rashin da’a a ofis.

Yadda dambarwar jami'in ta fara a Equatorial Guinea

An kuma ce an kori Engonga ne saboda halayyar iyali da zamantakewar da ya nuna da ake ganin bai dace da rike mukamin gwamnati ba.

Dambarwar Engonga ta fara ne bayan bullar wasu tarin fayafayan bidiyo sun nuna shi yana lalata da wasu manyan mata da 'yan uwansa, a cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Sweden: Kotu ta daure dan gwagwarmaya a gidan kaso kan kona Alkur'ani, ya yi martani

Bullar wadannan bidiyo a shafukan sada zumunta ya jawo ce-ce-ce-kuce, inda uwargidan shugaban kasar Equatorial Guinea, Constancia Mangue Obiang ta yi Allah wadai.

Engonga: An cafke jami'in gwamnati

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta cafke shugaban hukumar binciken kudade ta kasar (ANIF), Baltasar Ebang Engonga.

An kama Baltasar Engonga, bayan bullar bidiyon da ke nuna yana lalata da wasu mata sama da 400, daga cikinsu akwai wadanda ke auren manya a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.