Trump vs Harris: An Bayyana Wanda Ya Samu Nasara a Zaben Shugaban Kasar Amurka

Trump vs Harris: An Bayyana Wanda Ya Samu Nasara a Zaben Shugaban Kasar Amurka

  • Rahotanni mabambanta sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Donald Trump ne ya sake lashe zaben shugaban kasar Amurka
  • A ranar Talata, 5 ga Nuwamba ne aka kada kuri'u a kasar Amurka, inda Trump ya fafata da Kamala Harris da wasu 'yan takara
  • Wannan nasara da Trump ya samu, ta sa ya shiga tarihin kasar, na zama mutum na biyu da ya ci zabe sau biyu a lokuta daban daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Kafofin yada labarai sun bayyana cewa Donald Trump ne ya samu nasara a zaben shugaban kasar Amurka, inda ya doke Kamala Harris.

Wannan nasara da Donald Trump ya samu a zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar ranar Talata, ta girgiza kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Trump ya yi gaba a zaben Amurka, ya fara shinshino nasara kan Kamala Haris

Kafofin watsa labarai sun bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasar Amurka
Donald Trump ya samu nasara a zaben shugaban kasar Amurka. Hoto: @realDonaldTrump
Asali: Twitter

Donald Trump ya samu nasara a zaben Amurka

Kafar watsa labaran CNN a ranar Laraba ta ce Donald Trump 'ya samu nasara' a zaben shugaban kasar na 2024, wanda ya shiga tarihin siyasar kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar da Trump ya samu a Wisconsin ya sa 'yan Republican sun shiga gaba da kuri'u 277 na wakilan zabe yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'u a wasu muhimman jihohi.

Trump ya samu nasarar lashe zaben duk da abubuwan da suka faru da shi, kama daga zargin ta'addanci, yunkurin kashe shi da kuma gargadi daga tsohon shugaban ma'aikata.

Trump ya shiga tarihi a siyasar Amurka

Donald Trump zai koma fadar White House a matsayin shugaban kasa, bayan sauka daga kan mukamin shekaru hudu da suka gabata.

A shekarar 2020 ne Trump ya sha kaye a neman tazarcen da ya yi, inda aka yi zargin ya so murde zaben, da kuma fuskantar tsigewa daga kujerar shugaban kasa har sau biyu.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

Rahoton kafar labaran FOX ya nuna cewa Trump ya shiga tarihin siyasar Amurka inda ya zamo na biyu da ya lashe zabe sau biyu a lokuta daban daban.

Amurka: An fara murnar nasarar Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa magoya bayan Donlad Trump sun fara murna yayin da aka fara fitar da sakamakon zaben shugaban Amurka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ne a gaba yayin da Kamala Harris ke binsa a baya a yawan kuri'u.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.