An Fara Murnar Lashe Zaben Amurka, Trump Ya Buga Kamala Harris a Kasa
- Yayin da ake cigaba da samun rahotanni kan sakamakon zaben Amurka, magoya bayan Donald Trump sun fara murnar nasara
- A safiyar yau magoya bayan Donald Trump a Florida suka cika titunan jihar bisa ganin nasarar da Trump ke cigaba da samu
- A bisa sakamakon zaben da aka tattara, Donald Trump ne ke gaba da babbar abokiyar hamayyarsa watau Kamala Harris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Magoya baya sun fara murna yayin da aka fara fitar da sakamakon zaben shugaban kasa a Amurka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ne a gaba yayin da Kamala Harris ke binsa a baya.
Rahoton ABC News ya nuna cewa magoya bayan Trump sun fara murnar lashe zaben bisa alamun da suka gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana murnar lashe zaben Donald Trump
Magoya bayan Donald Trump a jihar Florida sun fara murnar samun nasara yayin da aka fara fitar da sakamakon zabe.
Lura da sakamakon da aka tattara, Donald Trump ya sha gaban babbar abokiyar hamayyarsa, Kamala Harris da kuri'u sosai.
Maza da mata ne dauke da hotunan Trump suka taru a dandalin Beach County suna rawa da ihu bisa nasarar da suka hango.
Maganar magoya bayan Trump
Magoya bayan Donald Trump sun bayyana cewa tun farko sun ga alamar nasara kuma sakamakon zabe na tabbatar da abin da suka yi hasashe.
"Na ji a raina Trump zai yi nasara kuma ina da tabbacin cewa za a samu sauyi a duniya."
-Moses Abraham, dan shekaru 22
"Kamar dai zaben 2016, wannan karon ma Trump zai yi nasara. Donald Trump ne ya dace ya shugabanci Amurka a yanzu."
-Jo Ann Poly Calvo
Jaridar Punch ta wallafa cewa magoya bayan Trump sun ce an mayar da Amurka baya a karkashin Joe Biden shi ya sa suka zabi Trump.
Trump: Jam'iyyar Republican ta yi gaba a majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta Republican ta lashe manyan kujeru a majalisar dattawan Amurka.
Hakan na nufin Republican na shirin karbe shugabancin majalisar dattawa a Amurka bayan lashe kujerun sanatoci a Ohio da West Virginia.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari
Asali: Legit.ng