Trump v Kamala: Yadda Ake Zaben Wanda Zai Zama Shugaban Kasa a Amurka

Trump v Kamala: Yadda Ake Zaben Wanda Zai Zama Shugaban Kasa a Amurka

A ranar Talata, 5 ga watan Nuwamban 2024, Amurkawa za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, inda za su zaɓi tsakanin ƴar takarar jam'iyyar Democrat, Kamala Harris da na Republican, Donald Trump.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Zaɓen wanda duniya ke sa ido a kansa, ya kuma haɗa da zaɓen ƴan majalisar dokoki, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara dokokin Amurka.

Yadda ake zaben Amurka
Donald Trump da Kamala Harris ne kan gaba a takarar shugaban kasan Amurka Hoto: Kamala Harris, Donald J. Trump
Asali: Facebook

Wanda ya yi nasara zai yi aiki na tsawon shekaru huɗu, inda wa'adin mulkinsa zai fara daga watan Janairun 2025, shafin Usa.gov ya tabbatar da wannan.

Su waye ƴan takara a zaɓen Amurka?

A jam'iyyar Republican, tsohon shugaban ƙasa, Donald Trump ya zama wanda ya samu tikitin takara, ya zaɓi sanatan jihar Ohio, JD Vance a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara yi wa PDP illa, tsohon ɗan Majalisa da wasu jiga jigai sun koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamala Harris, mataimakiyar shugaban ƙasa na yanzu, ta zama ƴar takarar jam'iyyar Democrat, bayan Shugaba Joe Biden ya yanke shawarar haƙura da yin takara.

Abokin takararta shi ne gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz.

Akwai kuma ƴan takara masu zaman kansu, ciki har da Robert F. Kennedy Jr., ko da yake ya janye a watan Agusta sannan ya goyi bayan Donald Trump.

Yadda zaɓen Amurka ke aiki

Ƙasar Amurka na amfani da tsarin wakilan masu zaɓe (Electoral College) maimakon yawan ƙuri'un da aka kaɗa.

Wannan yana nufin ɗan takarar da ya samu mafi yawan ƙuri'u a zaɓen ba lallai ne ya zama wanda ya yi nasara ba.

Kowace jiha ta Amurka ana ba ta adadin wakilan masu zaɓe takamaiman wakilcin da take da shi a majalisa.

Wannan tsarin ya ƙunshi ƙuri'u biyu na sanatocin kowace jiha da ƙarin ƙuri'u daidai da adadin gundumomin majalisa a cikin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa illa, sun hallaka surukarsa da dan uwan matarsa

Akwai jihohi 50 a Amurka waɗanda ke da ƙuri'un wakilan masu zaɓe 538, sannan ɗan takara yana buƙatar samun ƙuri'u 270 domin ya yi nasara.

Jihohi kamar Alaska, Vermont, da Wyoming suna da masu jefa ƙuri'un wakilan masu zaɓe guda uku kawai, yayin da Florida ke da 30. California, jihar da ta fi yawan jama'a, tana da mafi yawan ƙuri'u 54.

Jihohin da za a fafata a zaɓen Amurka

Yayin da jihohi da dama sun saba kaɗa ƙuri'unsu ga Democrat ko Republican, wasu jihohin da aka fi sani da "swing" ko filin daga na iya raba ƙuri'unsu.

Ƴan takarar suna maida hankali wajen yaƙin neman zaɓensu a irin waɗannan jihohin domin ganin sun samu ƙuri'u.

CBS News ta ce waɗannan jihohin a zaɓen shugaban ƙasa na 2024 su ne, Arizona, Georgia, Michigan, Nevada, North Carolina, Pennsylvania, da Wisconsin.

Ɗan takara zai iya rasa mafi yawan ƙuri'un da jama'a suka kaɗa amma ya yi nasara ta hanyar ƙuri'un wakilan masu zaɓe kamar yadda ya faru a 2016 lokacin da Trump ya yi nasara duk da cewa Hillary Clinton ta fi samun yawan ƙuri'u.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

Shugabannin Amurka biyar kawai suka taɓa yin nasara ba tare da samun mafi yawan ƙuri'u ba, inda uku daga cikinsu an yi su ne a ƙarni na 19.

Me zai faru idan aka yi kunnen doki?

Idan babu ɗan takarar da ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 270, sannan aka samu kunnen doki 269-269, majalisar wakilai ke yanke hukuncin ƙarshe a abin da ake kira "zaɓen wucin gadi."

Idan aka samu kunnen doki wanda hakan zai sanya majalisa ta yi zaɓen, wakilan kowace jiha a majalisar suna da ƙuri'a ɗaya, sannan ɗan takarar da ya samu mafi yawan jihohi ne zai zama shugaban ƙasa.

Daga nan sai majalisar dattawa ta zaɓi mataimakin shugaban ƙasa, inda kowane sanata zai kaɗa ƙuri'a ɗaya.

Wannan tsarin na iya samar da shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa daga jam'iyyu daban-daban.

Hakan na nufin zai iya yiwuwa Trump ya zama shugaban ƙasa sannan Tim Walz na Democrat ya zama mataimakinsa, ko Kamala Harris ta zama shugabar ƙasa sannan JD Vance na Republican ya yi mata mataimaki.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu

Idan har akwai buƙatar a yi irin wannan zaɓen na majalisa, za a gudanar da shi ne a ranar, 6 ga watan Janairun 2026.

Trump ya magantu kan zaɓen Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump ya yi iƙirarin cewa za a yi wani babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya idan bai ci zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba mai zuwa ba.

Donald Trump ya kuma cewa akwai yiwuwar za a yi "yaƙin duniya na uku" idan bai koma kan kujerar mulkin ƙasar Amurka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng