Bayan Kashe Nasrallah da Isra'ila Ta Yi, Hezbollah Ta Nada Sabon Shugaba

Bayan Kashe Nasrallah da Isra'ila Ta Yi, Hezbollah Ta Nada Sabon Shugaba

  • Kungiyar Hezbollah ta sanar da nadin sabon jagora da zai maye gurbin Hassan Nasrallah da Isra'ila ta kashe a Beirut
  • Hezbollah ta nada Naim Qassem a matsayin Sakatare Janar, wanda zai ci gaba da jagorantar kungiyar a fafutukar da ta ke yi
  • Amma har yanzu babu tabbacin wurin da sabon jagoran ke da zama, ana hasashen cewa ya na boye a kasar Iran da ke mara masu baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Lebanon – Hezbollah ta sanar da sabon Sakatare Janar da zai jagorance ta bayan kisan tsohon shugaban kungiyar, Hassan Nasrallah.

Dakarun Isra’ila sun kashe Nasrallah a wata ranar Juma’a bayan wani mummunan hari da dakarun IDF su ka kai Beirut.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata ya yi magana da ya ji labarin manyan Arewa sun yi zama

Hezbollah
Hezbollah ta nada sabon shugaba Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Kafar Aljazeera ta wallafa cewa Hezbollah ta fitar da sanarwar cewa sabon jagoranta ya cika dukkanin sharuda da dokokin da kungiyar ta aminta da su bisa dokar musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hezbollah ta nada sabon shugaba

BBC Hausa ta ruwaito cewa Hezbollah ta nada Naim Qassem a matsayin jagora a kungiyar, inda aka nada shi Sakatare Janar.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta yi addu’ar Allah SWT zai yi wa Naim Qassem jagoranci a fafutukar da su yi har sai an kai ga nasara, tare da yin addu’ar samun rahama ga tsohon shugabanta, Hassan Nasrallah.

Hezbollah ta yi mubaya’a ga sabon shugabanta

Kungiyar Hezbollah ta jaddada mubaya’a ga sabon jagoranta, Naim Qassem da ya maye gurbin jagoranta, Hassan Nasrallah da sojojin Isra’ila su ka kashe a kwanakin baya.

Duk da sanar da nadin nasa, babu wanda ya san wurin da sabon shugaban ke zaune ba, amma ana hasashen cewa ya na zaune a Iran da ke taimakawa kungiyar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ragargaji Tinubu, ya fadi yadda rashin wuta zai yi wa Arewa

Dakarun Hezbollah sun kora sojojin Isra'ila

A baya mun ruwaito cewa dakarun Hezbollah sun bayyana nasarar da su ke samu wajen dakile yunkurin da sojojin IDF na Isra'ila su ka yi na kutsawa cikin kasar Lebanon ta iyakokinta.

Amma kasar Isra'ila, karkashin jagorancin Benjamin Netanyahu ta gargadi mazauna Lebanon da su gujewa goyon bayan dakarun Hezbollah, su barranta kansu da su, ko ta mayar da su kamar Gaza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.