Isra'ila Ta Kai Hare Hare kan Kasar Iran, an Samu Bayanai

Isra'ila Ta Kai Hare Hare kan Kasar Iran, an Samu Bayanai

  • Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya kan ƙasar Iran a wani yunƙuri na ƙara takalar faɗa a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ƙasar Iran ta tabbatar da kai hare-haren a kan sansanonin soji da ke wasu larduna guda uku na ƙasar ciki har da birnin Tehran
  • Amurka ta tabbatar da kai hare-haren inda ta gargaɗi Iran da ka da ta kuskura ta ce za ta rama harin da Isra'ila ta kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Iran - Isra'ila ta kai hare-hare ta sama kan Iran a cikin dare a birnin Tehran babban birnin ƙasar da kuma sansanonin soji a aƙalla wasu sassa biyu na ƙasar.

Ƙasar Iran ta ce hare-haren ba su yi mata wata ɓarna mai yawa ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi adawa da yi wa dokar shari'ar Muslunci kwaskwarima a kundin tsarin mulki

Isra'ila ta kai hari a Iran
Isra'ila ta kai hare-hare a Iran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Isra'ila ta kai hari kan Iran

Jaridar Aljazeera ta rahoto cewa sojojin Isra'ila sun kai hare-hare kan Iran, inda suka kai hari a kusan wurare 20 cikin sa'o'i da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-haren dai wani martani ne ga harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan Isra'ila a ranar 1 ga watan Oktoban 2024.

Wani mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya ce harin wanda ya yi wa laƙabi da "Days of Reckoning" an kai shi ne domin farmakar damar da Iran take da ita ta ƙera makamai masu linzami.

Me Iran ta ce kan harin?

Sojojin ƙasar Iran sun tabbatar da harin da Isra'ila ta kai kan sansanonin soji da ke lardunan Ilam, Khuzestan da Tehran, inda suka ce ba su yi wata ɓarna mai yawa ba.

Israel ta gargaɗi Iran kan maida martani inda tace zai zama wajibi a gareta ta sake kai hari idan Iran ta rama, inda ta ƙara da cewa tana da sauran wurare da dama da za ta farmaka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da manoma, sun sace kayan abinci

Me Amurka ta ce kan harin?

Wani kakakin tsaron Amurka ya ce fadar Washington na sane da hare-haren da Israila ta kai amma babu hannunta a ciki, inda ya ƙara da cewa harin da Isra'ila ta kai na kare kanta ne.

Fadar White House tace harin ya kamata ya kawo ƙarshen musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila inda ta gargaɗi Iran da cewa za ta kuka da kanta idan ta rama.

Amurka ta gargaɗi Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Amurka ta bayyana cewa lokaci ya yi da Isra'ila za ta tsagaita wuta tare da kawo karshen kashe Falasdinawa da ke zaune a Zirin Gaza.

Sakataren gwamnatin Amurka, Anthony Blinken ne ya bukaci haka, inda ya kara da cewa dakarun Isra'ila sun cimma nasarar da su ke buƙata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng