Amurka ta Gaji, Ta Bukaci Israila Ta Kawo Karshen Kashe Mutane a Gaza

Amurka ta Gaji, Ta Bukaci Israila Ta Kawo Karshen Kashe Mutane a Gaza

  • Bayan shafe akalla shekara guda Isra'ila na luguden wuta a kasar Falasdinu, Amurka ta ce lokacin kawo karshen yakin ya yi
  • Sakataren wajen Amurka, Anthony Blinken ne ya bayyana haka a lokacin da ake zargin kasarsa da bayar da makamai ga Isra'ila
  • Anthony Blinken ya ce kasar Isra'ila ta cimma nasarori sosai bayan hare haren da ta kai ya kashe yan ba ruwa ba da dakarun Hamas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar America - Kasar Amurka ta bayyana cewa lokaci ya yi da Isra'ila za ta tsagaita wuta tare da kawo karshen kashe Falasdinawa da ke zaune a Zirin Gaza.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Sakataren gwamnatin Amurka, Anthony Blinken ne ya bukaci haka, inda ya kara da cewa dakarun Isra'ila sun cimma nasarar da su ke bukata.

Anadolu
Amurka ta nemi kawo karshen yaki a Gaza Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Jaridar Reuters ta bayyana cewa Anthony Blinken ya fadi haka ne a lokacin da ya ke shirin tafiya birnin Riyadh a ziyarar da ya ke kai wa kasashen Gabas ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin bukatar Amurka na daina yakin Gaza

Tashar RFI ta ruwaito cewa Sakataren Amurka, Anthony Blinken ya ce Isra'ila ta yi nasarar rugurguza Hamas a matsayin kungiya mai karfin soji.

Ya kara da cewa kashe Yahya Sinwar babbar nasara ce da Isra'ila ta samu bayan ta kashe mutane da dama.

A cikin wadanda aka kashe har da yara jarirai, kananan yara, matasa da mazan da babu ruwansu da yakin.

Shirin ƙasar Amurka kan Gaza

Anthony Blinken ya ce yanzu lokaci ne na samar da Gaza da kungiyar Hamas ko Isra'ila ba ta da hurumin juyawa bayan shafe akalla shekara guda ana ragargazar yankin.

Kara karanta wannan

"Sun zama maboyar miyagu:" FCTA ta bayar da wa'adin kammala gine gine a Abuja

Sakataren Amurka na ganin lokaci ya yi na kawo karshen yakin da ya kori Hamas daga Gaza, tare da tabbatar da cewa Isra'ila ba ta rika iko da Zirin ba.

Isra'ila ta tsokano yaki a Gaza

A baya mun ruwaito cewa dakarun sojojin IDF na kasar Isra'ila sun kara kai hari Arewacin Gaza da ke kasar Falasdina inda ta ke luguden wuta a kokarinta na fatattakar mayakan Hamas.

Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce dakarunta sun kai harin da ya yi sanadiyyar kashe shugaban gwamnatin Hamas a zirin Gaza, Rawdhi Mushtah da wasu daga cikin kusoshin kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.