Sanatoci Sun Tsige Mataimakin Shugaban Kasa Yana Jinya a Kenya, Bayanai Sun Fito

Sanatoci Sun Tsige Mataimakin Shugaban Kasa Yana Jinya a Kenya, Bayanai Sun Fito

  • An tsige mataimakin shugaban kasar Kenya, Rigathi Gachagua bayan samunsa da aikata laifuffuka biyar cikin 11 da ake tuhumarsa
  • Majalisar dattawan kasar ta kada kuri'ar tsige Rigathi Gachagua a ranar Alhamis, lamarin da ba a taba gani irinsa ba a kasar Kenya
  • Tuhume tuhumen da ake yi wa Gachagua wadanda ya musanta, sun hada da cin hanci da rashawa, halatta kudin haram da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kenya - Majalisar dattawan Kenya ta tsige mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua ta hanyar kada kuri'a a ranar Alhamis, 17 ga Oktobar 2024.

Majalisar ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar bayan samunsa da aikata laifuffuka biyar cikin 11 da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Direbobin da ke bin babbar hanya a Arewa za su fara biyan haraji a sabon tsari

Majalisar dattawa ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar Kenya, Rigathi Gachagua
Majalisa ta tsige mataimakin shugaban kasar Kenya ta hanyar kada kuri'a. Hoto: @rigathi
Asali: Twitter

Kenya: An tsige mataimakin shugaban kasa

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa majalisar dattawan na bukatar samunsa da aikata laifi daya kacal domin tsige Rigathi Gachagua daga mukaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shi ne mataimakin shugaban kasa na farko da aka tsige ta wannan hanya tun bayan gabatar da 'dokar tsige masu mulki' a kundin tsarin mulkin Kenya na shekarar 2010.

A cewar kakakin majalisar dattijai, Amason Kingi, "wannan na nufin cewa mai girma Rigathi Gachagua ba ya rike da wani ofishi a yanzu."

Ina dalilin tsige mataimakin shugaban Kenya?

Sanatoci 54 daga cikin 67 ne suka kada kuri'ar tsige Gachagua bisa tuhumar farko da ake yi masa na "cin zarafin kundin tsarin mulkin kasar."

Tuhume Tuhume 11 wadanda Gachagua ya musanta sun hada da cin hanci da rashawa, rashin biyayya ga kundin mulki, halatta kudin haram da kuma zagon kasa ga gwamnati.

Kara karanta wannan

'Alamar matsala tsakanin Tinubu da Shettima,' Hadimin Osinbajo ya fito da bayanai

Sauran tuhume tuhumen sun hada da yin siyasa mai raba kan kabilu, cin zarafin jami’an gwamnati da yin barazana ga alkali, inji rahoton Reuters.

An dakatar da ministocin Kenya

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasar Kenya, William Ruto ya sallami daukacin majalisar ministocinsa baya amma ya kyale ministan harkokin wajen kasar.

Shugaba Ruto ya kori ministocin ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a fadin kasar na tsawon makonni wanda ta jawo asarar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.