Majalisar Tarayya ta kawo dokar da za ta halasta tsige Shugaban kasa daga hawansa mulki

Majalisar Tarayya ta kawo dokar da za ta halasta tsige Shugaban kasa daga hawansa mulki

- Watakila kin kafa gwamnati da wuri zai zama laifi a tsarin mulki da dokokin kasa

- Majalisar Wakilai ta kawo kudirin da zai sa a tsige Shugaban kasa idan ya yi nawa

- Idan aka shafe wata ba a nada Ministoci ba, Majalisa na so ta tsige shugaban kasa

Wani kudiri da zai bada damar a sauke shugaban kasar Najeriya daga kan mulki idan har ya yi kwanaki 30 a ofis bai nada Ministoci ba, yana samun shiga.

Jaridar The Cable ta ce wannan kudirin ya tsallake mataki na biyu a zaman majalisar wakilai.

An yi wa wannan kudiri take da ‘Transition and Assumption Bill 2020’, wanda zai ba ‘yan majalisar tarayyar ikon tsige shugaban kasa daga kujerarsa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun aukawa garin Batsari sun kai hari

Wani sashe na kudirin ya ayyana kin kafa gwamnati a matsayin sakaci daga fadar shugaban kasa, idan abin ya kai wata daya, za a tsige shugaban kasa.

Sashe na 19(1) na kudirin yake cewa: “Da zarar shugaban kasa ya shiga ofis, ya zama masa dole ya nada Ministocinsa, bayan kwanaki 30 da yin rantsuwarsa.”

Sannan sashe na 19(2) ya ce: “Shugaban kasa zai nada duk majalisar da ke sa ido a kan hukumomi da cibiyoyin gwamnati, watanni biyu da hawansa mulki.”

Har ila yau, sashe na 19(3) ya ce: “Za a samu shugaban kasa da babban laifi, kamar yadda sashe na 143(2)(b) na kundin tsarin mulki ya kawo, idan ya saba doka.”

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo ya yi magana a kan 2023

Majalisar Tarayya ta kawo dokar da za ta halasta tsige Shugaban kasa daga hawansa mulki
Ana zaman Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Wannan sashe ya bada dama majalisa ta sauke shugaban kasa, a nada mataimakinsa ko wani, idan aka same shi da aikata laifi ko ya gagara sauke nauyinsa.

Jaridar Premium Times ta rahoto mataimakin shugaban marasa rinjaye, Toby Okechukwu, ya na cewa kudirin zai sa a daina bata lokaci wajen nada Ministoci.

Sai wannan kudiri ya je gaban shugaban kasa, sannan zai iya zama doka a karkashin tsarin mulki.

Idan muka koma kan siyasar 2023, za mu ji kungiyar Osinbajo Grassroots Organisation ta hakikance a kan sai Yemi Osinbajo ya yi takarar Shugaban kasa.

Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, Farfesa Yemi Osinbajo ya saba cewa ba ya harin kujerara Mai gidansa, amma duk da haka, wasu suna kara tallata takararsa.

r

Asali: Legit.ng

Online view pixel