Dakarun Hezbollah Sun Kora Sojojin Isra'ila daga Iyakokin Kasar Lebanon

Dakarun Hezbollah Sun Kora Sojojin Isra'ila daga Iyakokin Kasar Lebanon

  • Mayakan Hezbollah sun bude wuta a yakin da ke gudana tsakanin kungiyar da Isra'ila, wannan karon ma ta lallasa sojojin kasar
  • Kungiyar ta bayyana cewa ta dakile yunkurin wasu daga cikin sojojin Isra'ila na kutsawa cikin Lebanon ta iyakokin kasar
  • Isra'ila na cigaba da da gargadin jama'a kan Hezbollah, inda ta bayyana cewa mazauna kasar su gaggauta yi wa kungiyar bore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Lebanon – Kungiyar fafutuka ta Hezbollah ta bayyana cewa ana kara samun nasarori kan sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa Lebanon.

Ta ce dakarunta sun yi namijin kokari wajen dakile karfin ikon sojojin Isra’ila a iyakar Lebanon da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Hezbollah
Dakarun Hezbollah sun fatattaki sojojin Isra'ila Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

BBC ta wallafa cewa mayakan kungiyar sun fatattaki sojojin Isra’ila daga Gabashi da Yammacin Lebanon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun Hezbollah sun farmaki sojojin Isra’ila

Jaridar Reuters ta tattaro cewa sojojin kungiyar Hezbollah sun fatattaki dakarun Isra’ila daga iyakar Lebanon.

Sojojin sun kai harin kwantan bauna kan dakarun Isra’ila da ke kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon ta gabashin kasar.

Kungiyar Hezbollah ta kori dakarun Isra’ila

Jim kadan bayan kashe wasu daga cikin jagororinta, kungiyar Kezbollah ta ce ta yi nasarar kora sojojin Isra’ila da ke son shiga Lebanon.

An kora sojojin ne ta iyakokin kasar ta bangaren Kudu da Yamma tare da jikkata wasu guda biyu a ranar Talata.

Isra'ila ta yi shiru kan harin Hezbollah

Kawo yanzu kasar Isra'ila ba ta ce komai kan hare-haren da kungiyar Hezbollah ta ce ta kai kan dakarun sojojin kasar ba.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Dattawan Arewa za su nemo hanyar magance matsalar tsaro

Sai dai an ji Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya gargadi mazauna Lebanon da su yi wa Hezbollah bore ko a mayar da kasarsu kamar zirin Gaza.

Hezbollah ta kai harin rokoki a Isra'ila

A baya mun wallafa cewa dakarun Hezbollah sun bayyana kai hare-haren kan sansanin makaman Isra'ila da ke Arewacin kasar ta hanyar zuba masu ruwan rokoki ta sama.

An tabbatar da kai harin yankunan Dishon, Dalton da Yir'on tare da ragargaza makamansu, yayin da kasar Isra'ila ta tabbatar da cewa Hezbollah ta harba rokoki akalla 200 cikin kasarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.