Tinubu: Jerin Shugabannin Kasashen Afirka 11 da Suka Haura Shekaru 70 a Duniya

Tinubu: Jerin Shugabannin Kasashen Afirka 11 da Suka Haura Shekaru 70 a Duniya

Duk da cewa a baya-bayan nan an samu shugabanni matasa a Afirka, amma har yanzu Afrika na da shuagabannin da suka dade a kan mulki kuma suka haura shekaru 70 a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Waɗannan shugabanni su na da babban tasiri a siyasar ƙasashensu kuma suna ci gaba da jagorantar al'ummominsu ta hanyar sauye-sauye a fasaha da zamantakewa.

Jerin shugabannin kasashen Afrika da suka haura shekaru 70 a duniya
Tinubu da wasu shugabannin kasashen Afrika da suka haura shekaru 70 a duniya. Hoto: @DrNangoloMbumba, @PR_Paul_BIYA, @OfficialABAT
Asali: Twitter

A nan kasa akwai wasu shugabannin nahiyar Afrika 11 da suka haura shekaru 70 a duniya kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

1. Paul Biya: Kamaru

Paul Biya na kasar Kamaru shi ne mafi tsufa, yana da shekaru 91 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Tun a watan Nuwambar 1982 ya ke kan kujerar shugaban kasar Kamaru, wanda ya sa ya shiga sahun shugabanni mafi dadewa a kan mulki a duniya.

2. Nangolo Mbumba: Namibia

Nangolo Mbumba na kasar Namibia, mai shekaru 82, ya zama shugaban kasa bayan mutuwar shugaba Hage Geingob a watan Fabrairun 2024, inji rahoton Business Day.

3. Alassane Ouattara: Ivory Coast

Ouattara na kasar Ivory Coast, wanda shi ma ya na da shekaru 82 a duniya, ya kasance shugaban kasa tun daga shekarar 2010 kuma ya ba gudunmawa wajen bunkasa kasar.

4. Teodoro Mbasogo: Equatorial Guinea

Teodoro Nguema Mbasogo na kasar Equatorial Guinea mai shekaru 81, ya kasance shugaban kasa tun 1979 bayan ya hambarar da kawunsa a wani juyin mulki.

5. Emmerson Mnangagwa: Zimbabwe

Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabwe mai shekaru 81 a duniya, ya zama shugaban kasa tun watan Nuwamban 2017, bayan juyin mulkin da ya hambarar da Robert Mugabe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara rabawa matasa Keke Napep 2000 marasa amfani da fetur

6. Nana Akufo-Addo: Ghana

Nana Akufo-Addo na kasar Ghana, mai shekaru 79, ya kasance shugaban kasa tun a shekarar 2017 kuma ya mayar da hankali wajen magance cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki.

7. Joseph Boakai: Laberiya

An rantsar da Joseph Boakai mai shekaru 79 a matsayin shugaban kasar Laberiya a watan Janairun 2024, Boakai ya gaji George Weah mai shekaru 51.

8. Yoweri Museveni: Uganda

Yoweri Museveni na Uganda, mai shekaru 79, ya kasance shugaban kasar tun shekara ta 1986. Mulkinsa na cike da daidaito amma mai tarin kalubale.

9. Abdelmadjid Tebboune: Aljeriya

Abdelmadjid Tebboune na Aljeriya, mai shekaru 78, ya kasance shugaba tun daga Disambar 2019. Ya mayar da hankali kan kawo sauyi da kwanciyar hankali bayan rikicin siyasar kasar.

10. Ismail Omar Guelleh: Djibouti

Ismail Guelle na kasar Djibouti, shi ma dan shekaru 76, yana kan karagar mulki tun a shekarar 1999, kuma ya bunkasa kasar Djibouti a yankin Afirka.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

11. Bola Tinubu: Najeriya

An rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya a watan Mayun 2023. Ya cika shekaru 72 a ranar 29 ga Maris din 2024.

Biranen Afrika mafi yawan jama'a

A wani labarin kuma, mun rahoto maku manyan biranen kasashen Afrika da suka fi ko ina samun bunkasa a yawan al'umma a shekarar 2024.

A cikin jadawalin an bayyana cewa Alkahira da ke kasar Masar ce babban birni mafi yawan jama'a a Afrika, inda suke da mazauna miliyan 21.75.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.