Tarihi zai Maimaitu?: Yadda Aka Ragargaza Sojojin Isra’ila a Kasar Lebanon a 2006

Tarihi zai Maimaitu?: Yadda Aka Ragargaza Sojojin Isra’ila a Kasar Lebanon a 2006

  • A ranar Talata yaki ya fara kaurewa a gabas ta tsakiya yayin da kasar Iran ta kai zafafan hare haren ramakon gayya kan Isra'ila
  • Lamarin ya faru ne bayan kisan shugaban kungiyar Hisbullah, Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi bayan kai hari kasar Lebanon
  • A shekarar 2006 an gwabza fada tsakanin Isra'ila da Hisbullah a Lebanon inda aka yiwa sojojin Isra'ila jina jina a yayin yakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lebanon - Gabas ta tsakiya na neman rincaɓewa yayin da Iran ta kai zafafan hare hare kasar Isra'ila kan kashe shugaban Hisbullah.

Masana na ganin cewa tarihi ne zai iya maimaita kansa kamar yadda aka gwabza fada tsakanin Isra'ila da Hisbullah a Lebanon a 2006.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Yaki a Lebanon
Yadda aka gwabza da Isra'ila a Lebanon a 2006. Hoto: Yoav Lemmer
Asali: Getty Images

Rahotan Aljazeera ya bayyana cewa yakin da aka yi a shekarar 2006 bai yi wa Isra'ila kyau ba kuma an yi mata asara mai yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya sa Isra'ila kai hari Lebanon

Yan kungiyar Hisbullah da ke Lebanon sun cigaba da kai hare hare kasar Isra'ila domin neman tsagaita wuta kan yaki da take yi da Falasdinawa da ya dauki shekara

Hakan ya sa Isra'ila ta dauki matakin kai hare hare kasar Lebanon inda hakan ya jawo kisan shugaban Hisbullah, Hassan Nasrallah.

Yadda ka gwabza a Lebanon da Isra'ila

Sai dai masana na ganin yakin ba zai yi wa Isra'ila kyau ba idan ta ce za ta cigaba da kai hare hare Lebanon ta kasa.

A 2006 kasar Isra'ila ta kwashi kashi a hannun Hisbullah da suka fara yaki ta ƙasa a kasar Lebanon inda sojin Isra'ila 121 suka mutu.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi sababbin dokoki, ta hana mata hawa Keke Napep daga karfe 10

Haka zalika motocin yakin Isra'ila kimanin 20 aka wargaza yayin yakin kuma hakan ne yasa masana ke ganin tarihi zai maimaita kansa.

Bincike da aka yi bayan yakin ya nuna cewa sojojin Isra'ila ba su samu nasara ba kuma haka suka fita daga kasar Lebanon bayan yin asara mai girma.

Iran ta kai hari a kasar Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa a ranar Talata aka wayi gari da zafafan hare hare a Tel Aviv, babban birnin Isra'ila.

Kasar Iran ce ta dauki nauyin kai hare haren kuma ta bayyana dalilan da suka sanya ta daukar matakin a kan Isra'ila a wannnan lokacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng