Yadda Iran Ta Kai Zafafan Hare Hare kan Kasar Isra’ila

Yadda Iran Ta Kai Zafafan Hare Hare kan Kasar Isra’ila

  • Rahotanni na nuni da cewa a ranar Talata aka wayi gari da zafafan hare hare a Tel Aviv, babban birnin kasar Isra'ila
  • Kasar Iran ce ta dauki nauyin kai hare haren kuma ta bayyana dalilan da suka sanya ta daukar matakin a kan Isra'ila
  • An samu sabani tsakanin ƙasashen kan barnar da hare haren suka yi wa Israila kasancewar an samu bayanai mabanbanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Iran ta kai zafafan hare haren ramakon gayya kasar Isra'ila a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi nufin wargaza wasu wuraren sojin Isra'ila ne yayin kai hare haren.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Shugaban Iran
Iran ta kai hari Isra'ila. Hoto: @drpezeshkian
Asali: Twitter

Rahoton Aljazeera ya tabbatar da cewa kimanin makamai mai linzami 200 Iran ta harba kasar Isra'ila a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kai hari daga Iran zuwa Isra'ila

Kasar Iran ta bayyana cewa ta kai hare hare Isra'ila ne kan kashe shugaban Hisbullah, Hassan Nasrallah da aka yi.

Haka zalika Iran ta kara da cewa kisan shugaban Hamas, Isma'il Haniyeh da Iran ta yi na cikin dalilan kai harin.

Barnar da harin Iran ya yi a Isra'ila

Kasar Iran ta bayyana cewa daga cikin makamai masu linzami 200 da ta harba Isra'ila, guda 180 sun samu wuraren da ta nufa.

Iran ta bayyana cewa ta nufi wargaza wasu sansanonin soji ne a Isra'ila duk da cewa kasar Isra'ila ta ce harin bai yi barna sosai ba.

Iran ta gargadi kasar Isra'ila

Biyo bayan harin, shugaban kasar Iran, Masoud Pezeskhian ya gargadi Isra'ila inda ya ce ka da ta kuskura ta fara yaki da su.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Mosoud Pezeskhian ya wallafa a X cewa ya kamata Benjamin Netanyahu ya san cewa Iran ba za ta yarda da wani kaskanci ba.

Saudiyya ta yanke alaka da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta jaddada matsayarta na cewa ba za ta kulla huldar jakadanci da Isra'ila ba har sai kasar Falasdinu ta zamo mai 'yanci.

Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman ya ce Saudiya na son Falasdinu ta samu 'yanci da gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng