Saudiya ta Yanke Alakar Diflomasiyya da Isra'ila, Ta Bukaci 'Yancin Falasdinu

Saudiya ta Yanke Alakar Diflomasiyya da Isra'ila, Ta Bukaci 'Yancin Falasdinu

  • Kasar Saudiya ta jaddada matsayarta na cewa ba za ta kulla huldar jakadanci da Isra'ila ba har sai kasar Falasdinu ta zamo mai 'yanci
  • Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman ya ce Saudiya na son Falasdinu ta samu 'yanci da gabashin Kudus a matsayin babban birninta
  • Bayanin hakan ya fito ne a yayin bude taro na tara na majalisar Shura, a madadin Sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz Al Saud

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudiya - Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman ya bayyana cewa, Masarautar ba za ta kuma kulla huldar diflomasiyya da Isra'ila ba.

Yarima Mohammed ya ce alakar kasashen biyu za ta dawo ne kawai idan kasar Falasdinu ta samu 'yanci da gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta.

Kara karanta wannan

Bayan tallafin biliyoyi, gwamnatin Borno ta fitar da gudunmawar ambaliya da ta samu

Saudiya ta yi magana kan alakar diflomasiyya da kasar Isra'ila
Saudiya ta ce ba za ta kulla alakar diflomasiyya da Isra'ila ba har sai Falasdinu ta samu yanci. Hoto: @HRHPRINCE_MBS
Asali: Twitter

Sanarwar ta nuna wani muhimmin mataki da ke karfafa matsayar Saudiyar da ya dade a kan rikicin Isra'ila da Falasdinu, inji rahoton RFI.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saudiya na neman 'yancin Falasdinu

Bayanin hakan ya fito ne a yayin bude taro na tara na majalisar Shura, a madadin mai kula da masallacin Makkah da Madinah, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud.

Yarima Mohammed bin Salman ya ce:

"Cikin kakkausar murya muke kara jaddada matsayar Saudiya na yin Allah-wadai da kuma nuna kin amincewa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa mutanen Falasdinu.
"Masarautar ba za ta daina kokarinta na ganin cewa kasar Falasdinu ta zamo mai cin gashin kanta tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta ba."

Matsayar Saudiya kan kasar Isra'ila

Jaridar The Cable ta rahoto Yarima Mohammed ya jaddada matsayar Saudiya cewa:

"Masarautar ba za ta kulla huldar diflomasiyya da Isra'ila ba har sai kasar Falasdinu ta zamo mai cikakken 'yanci."

Kara karanta wannan

Wahalhalu sun tsananta a Najeriya, Abdulsalami ya ba Tinubu muhimmiyar shawara

"Har ila yau, Masarautar tana neman inganta tsaro da zaman lafiya na kasashen duniya, ta hanyar yin yunƙurin warware rikicin Yemen, Sudan, Libya, da sauransu."

Yarima mai jiran gadon ya bayyana manufofin Saudiya kan alakarta da kasashen waje, inda ya bayyana aniyar Masautar na yin aiki tare da dukkanin kasashe masu tasiri a duniya.

"Ba mu tare da Isra'ila" - Saudiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Saudiya ta musanta shiga sa hannu a kakkabo jiragen Iran marasa matuka a wani mummunan harin da ta kai wa kasar Isra’ila.

Majiya mai tushe daga Masarautar ta jaddada cewa Saudiya ba ta tare da Isra'ila a hare-haren da ta kaiwa Falasdinu wanda ya sabawa dokar kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.