Yadda Aka Tafkawa Ministar 'Yan Sanda Sata a Taron Jami’an Tsaro

Yadda Aka Tafkawa Ministar 'Yan Sanda Sata a Taron Jami’an Tsaro

  • Ministar yan sanda a kasar Birtaniya, Dame Diana Johnson ta hadu da sharrin barayi a yayin wani taron jami'an tsaron
  • An ruwaito cewa wasu barayi ne suka sace jakar hannun Dame Diana Johnson yayin da ta ke magana a kan illar sace sace
  • Karin rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi kokarin cafke wani mutum da ake zargi yana da hannu a cikin satar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

United Kingdom - Rahotanni da suka fito daga kasar Birtaniya na nuni da cewa an yi wa ministar yan sandar kasar sata.

Rundunar yan sandan kasar Birtaniya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce a halin yanzu ta dukufa da yin bincike.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: An tono gawar matashin da aka birne a daƙi, an kama mutum 1

Diana
An sace jakar minista a Birtaniya. Hoto: Aaron Chown
Asali: Getty Images

Jaridar the Mirror ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a otel din Chesford Grange yayin wani taron jami'an yan sanda.

An sace jakar ministar yan sanda

Yan sanda a kasar Birtaniya sun tabbatar da cewa an sace jakar hannun minista Dame Diana Johnson a yayin wani taro.

Jami'an tsaron yankin Warwickshire sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin da ake taron yan sanda.

Rahoton da BBC ta wallafa ya nuna cewa an sace jakar minista Dame Diana Johnson ne a yankin Kenilworth a Warwickshire.

An fara bincike kan sace jakar minista

Yan sandan kasar Birtaniya sun tabbatar da faruwar lamarin tare da kaddamar da bincike domin gano yadda aka sace jakar.

Yan sanda sun kama wani mutum dan shekaru 54 da ake zargi yana da hannu wajen sace jakar 'yar siyasar mai shekara 58.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yiwa matashi yankan rago da kwalba, ya mutu har lahira

Sai dai rundunar yan sanda ta bayyana cewa an ba da belin mutumin kuma za a cigaba da bincike bayan an sake shi.

An yada kanjamau ga mutane a Birtaniya

A wani rahoton, kun ji cewa bincike ya gano yadda aka yi amfani da gurbataccen jini ga marasa lafiya wajen yada cututtuka ga mutane a kasar Birtaniya.

Tsohon Alkali Mista Brian Langstaff ne ya gudanar da bincike domin gano badakalar da ta cinye rayuka tsawon shekaru masu yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng