An Cafke Pavel Durov Mai Kamfanin Telegram Ana Shirin Sanya 'Dogs' a Kasuwa

An Cafke Pavel Durov Mai Kamfanin Telegram Ana Shirin Sanya 'Dogs' a Kasuwa

  • Attajirin matashin ne mai kamfanin sada zumunta na Telegram, Pavel Durov, ya faɗa hannun hukumomi a ƙasar Faransa
  • Jami'an tsaro sun cafke Pavel Durov ne bayan ya sauka a filin jirgin sama na Bourget a daren ranar Asabar, 24 ga watan Agustan 2024
  • Hukumomi a ƙasar Faransa dai na zargin Telegram da zama wani dandali da ke bari ana aikata laifuka irinsu ta'addanci, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Faransa - Hukumomi a ƙasar Faransa sun cafke attajirin nan mai kamfanin Telegram, Pavel Durov.

An tsare Pavel Durov ne a tashar jirgin sama ta Bourget da ke kusa da birnin Paris a daren ranar Asabar, 24 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir: 'Yan sanda sun cafke masu zanga zanga, sun fadi dalili

An cafke Pavel Durov a Faransa
An Cafke mai kamfanin Telegram, Pavel Durov a Faransa Hoto: @durov
Asali: Twitter

An cafke Pavel Durov a Faransa

Pavel Durov, wanda ya taho daga ƙasar Azerbaijan cikin jirginsa an cafke shi ne bayan ya sauka a filin jirgin saman, cewar rahoton jaridar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pavel Durov mai shekara 39 a duniya, yana tare ne da dogarinsa da wata mata a lokacin da jami'an tsaro suka cafke shi.

Me yasa aka cafke Pavel Durov?

Hukumomi sun cafke Durov ne bisa wani umarnin kamu da ke da alaƙa da binciken ƴan sanda kan zargin rawar da Telegram ke takawa wajen aikata laifuka, rahoton jaridar Sky News ya tabbatar.

Hukumomi a Faransa na zargin Telegram da bari ana aikata laifuka irinsu ta'addanci, safarar miyagun ƙwayoyi, zamba da sauransu.

Ana zargin Durov da ƙin taka birki kan ayyukan laifi da ake aikatawa a Telegram.

Durov wanda asalinsa ɗan ƙasar Rasha ne amma yana da fasfo na ƙasar Faransa, yana fuskantar ɗaurin shekara 20 a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bankado adadin masu digirin bogi daga kasashen waje

Yadda Pavel Durov ya haifi ƴaƴa 100

A wani labarin kuma, kun ji cewa wanda ya ƙirƙiri dandalin Telegram, Pavel Durov ya fallasa wani sirri mai ban mamaki game da haihuwar yara 100 da ya ce ya yi duk da bai taba yin aure ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Telegram, ɗan kasuwan mai shekaru 39 ya ba da labarin yadda ya kai ga haihuwar ‘ya’ya da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng