Bayan 'Gano' Albashin Sanatocin Najeriya, 'Dan Majalisar Amurka Ya Gargadi Tinubu

Bayan 'Gano' Albashin Sanatocin Najeriya, 'Dan Majalisar Amurka Ya Gargadi Tinubu

  • Dan majalisar Amurka, Beroro Efekoro ya turo gargadi ga gwamnatin Najeriya bayan gano albashin 'yan majalisar dattawa
  • Beroro Efekoro ya ce yadda yan majalisar Najeriya ke diban kudi da sunan albashi da alawus ya wuke yadda hankali zai dauka
  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne ya fara tono zance, ya ce 'yan majalisar Najeriya ke yankewa kansu kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Maganar albashi da alawus din yan majalisar dattawan Najeriya na cigaba da jan hankulan al'ummar duniya.

Wani dan majalisa a kasar Amurka, Beroro Efekoro ya nuna takaici kan yadda Sanatocin Najeriya ke samun kudi sosai da sunan albashi da alawus.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fito da salon tsarin tsaro a Arewa domin maganin yan bindiga

Beroro
Dan majalisar Amurka ya yi magana kan albashin Sanatocin Najeriya. Hoto: @realbte
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Beroro Efekoro ya bayyana lamarin ne a birnin New York da ke kasar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Beroro: "'Yan siyasar Najeriya suna cutar talaka"

The Nation ta wallafa cewa dan majalisar kasar Amurka, Beroro Efekoro ya ce gwamnatin Najeriya da yan siyasa suna suna son kai talaka bango.

Beroro Efekoro ya fadi haka ne kan yadda yan siyasa ke wadaka da dukiya alhali talakawa na fama da yunwa da talauci.

Kiran 'dan majalisar ga gwamnatin Tinubu

Dan majalisar ya ce akwai bukatar gwamnatin Tinubu ta fito da manufofinta fili ta yadda za ta gamsar da yan kasa.

Ya kuma kara da cewa gamsar da yan kasa ne kawai zai hana juyin juya hali da alamunsa suka bayyana a Najeriya.

Beroro ya tura sako ga shugaban majalisa

Beroro Efekoro ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya nisanci yin barazana ga Sanatoci da suke sukar gwamnati.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya ta janye kudirin daure marasa rera taken Najeriya a gidan yari

Ya ce bai kamata a ce majalisar dattawa ta zama 'yar amshin shatar gwamnatin tarayya ba matuƙar ana son kawo cigaba.

Majalisa ta musanta biyan albashin N21m

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta musanta ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da alawus-alawus duk ƙarshen wata.

Kakakin majalisar, Adeyemi Adaramodu ya bayyana cewa kudin da Sanata Kawu Sumaila ya yi iƙirarin ana ba shi ba albashi ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng