Tinubu Ya Kuma Gamuwa da Cikas Bayan Kwace Jiragen Fadar Shugaban Kasa 3 a Ketare

Tinubu Ya Kuma Gamuwa da Cikas Bayan Kwace Jiragen Fadar Shugaban Kasa 3 a Ketare

  • Gwamnatin Tarayya ta gamu da cikas bayan kwace jiragen samanta har guda uku da aka yi a kasashen ketare
  • Wata kotu ta ba da umarnin kwace jiragen a kasar Faransa bayan shigar da korafi da kamfanin Zhongshan na China ya yi
  • Daga cikin jiragen da aka cafke akwai biyu da aka yi gwanjonsu sai kuma daya wanda ba a dauko shi zuwa Najeriya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Paris, France - Wata kotu a kasar Faransa ta umarci kwace jiragen saman fadar shugaban Najeriya guda uku.

Biyu daga cikin jiragen saman su ne wadanda aka saka a kasuwa yayin daya an siya amma ba a kawo shi ba.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi bayan kotun turai ta saka Najeriya a gaba kan jirage 3

An kwace jiragen saman shugaban kasa, Tinubu a kasashen ketare
Wata kotu a Faransa da kwace jiragen saman fadar shugaban kasar Najeriya guda 3. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Takun-saka tsakanin kamfanin Zhongshan da gwamnati

Premium Times ta tabbatar cewa hakan bai rasa nasaba da korafin kamfani kasar China mai suna Zhongshan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin na takun-saka da gwamnatin jihar Ogun tun shekaru da suka wuce bayan ta kwace lasisinsa a jihar.

Kotu karkashin jagorancin tsohon shugaban Kotun Kolin Birtaniya ta ci tarar gwamnatin Ogun $74m amma ta ki bin umarnin.

Jiragen da aka kwace na shugaban kasa

Daga cikin jiragen da aka kwace akwai Dassault Falcon 7X a filin jirgin saman Le Bourget a Paris da Boeing 737 da kuma Airbus 330 a filin jirgin saman Switzerland.

Kotun ta ba da umarnin dakatar da siyarwa ko tafiya da jiragen har sai an biya kudin da aka ci tarar gwamnatin ba tare da baya lokaci ba.

Sai dai har zuwa yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani kan wannan rigima da ake ciki ba tukun.

Kara karanta wannan

Babu haraji: Bayani dalla dalla kan sharuddan shigo da abinci Najeriya kyauta

Gwamnati za ta sayawa Tinubu jirgin sama

Kun ji cewa gwamnatin Najeriya tana shirin sayo jiragen sama domin zirga-zirgar Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima a fadar shugaban kasa.

Jami’an fadar shugaban kasa sun yi gum game da batun bayan an koka cewa jiragen fadar shugaban kasa sun samu matsala, an sa su a kasuwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana kokarin sayen jirgin saman Airbus A330 a hannun wani attajirin balarabe a kasar waje cikin sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.