Joe Biden ya Fadi Masifar da za ta iya Aukuwa a Amurka kan Takarar Trump

Joe Biden ya Fadi Masifar da za ta iya Aukuwa a Amurka kan Takarar Trump

  • Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yi magana kan illar zaben abokin hamayyar jam'iyyarsa, Donald Trump a zaben Amurka mai zuwa
  • Shugaba Joe Biden ya yi bayanin ne yayin da siyasar Amurka ke kara daukan zafi tsakanin manyan yan takara, Donald Trump da Kamala Harris
  • Haka zalika Joe Biden ya yi karin haske kan lafiyar jikinsa da ake tunanin ita ce ta saka shi janye takara da ya fara shirin yi domin zabe karo na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya gargadi Amurkawa kan Donald Trump a zabe mai zuwa a kasar.

Joe Biden ya ce akwai matsalolin da Amurka za ta fuskanta matuƙar Donald Trump ya lashe zabe a kasar ko ya fadi.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya fadi yadda Tinubu zai magance matsalolin Najeriya

Joe Bide|Trump
Joe Biden ya fadi illar takarar Donald Trump. Hoto: Joy Raedel
Asali: Getty Images

Yahoo News ta wallafa cewa Joe Biden ya nuna gamsuwa kan yar takarar jam'iyyarsu, Kamala Harris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben Trump: Masifar da ke gaban Amurka

Rahoton Washinton Post ya nuna cewa Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yi ikirarin cewa idan Donald Trump ya ci zaɓe zai zama barazana ga tsaron Amurka.

Haka zalika Biden ya ce Trump zai iya tayar da rikici idan ya fadi zabe kamar yadda yake cewa idan bai ci zaɓe ba za a yi kare jini biri jiji.

Saboda haka shugaba Joe Biden ya ce Trump ya zama barazana ga Amurka da za a iya shiga masifa ko ya ci zabe ko ya fadi.

'Ina da cikakkiyar lafiya' - Biden

Shugaban kasa Joe Biden ya ce mutane suna masa kallon kamar ba shi da lafiya amma a hakikanin gaskiya lafiya kalau yake.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisa ya magantu kan farmaki yayin taro da Aminu Ado ya halarta

Ya kara da cewa a lokacin da ya yi muhawara kan tsayawa takara ba ya jin dadi ne amma babu wani rashin lafiya mai tsanani a tattare da shi.

A karshe, Joe Biden ya nuna karfin gwiwa kan jarumtar Kamala Harris wajen jagorantar ƙasar Amurka idan ta samu nasara a zabe mai zuwa.

Sojin Amurka sun fice daga Nijar

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Amurka ta sanar da ta fara janye dakarunta da suka kafa sansani a Nijar biyo bayan bukatar da kasar ta yi a baya.

A cikin shekaru sama da 10 kasar Nijar ta kasance wajen da Amurka ke kafa sansanin soji domin shirin yaki da ta'addanci a yankin Afrika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng