Matsala Ta Sake Kunno Kai a Gwamnatin Iran Bayan Kisan Shugaban Hamas

Matsala Ta Sake Kunno Kai a Gwamnatin Iran Bayan Kisan Shugaban Hamas

  • Mataimakin shugaban ƙasan Iran, Mohammed Javad Zarif, ya yanke shawarar yin murabas daga kan muƙaminsa a gwamnatin Shugaba Massud Pezeshkian
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Iran ya yi murabus ɗin bayan kwanaki 11 da rantsar da shi a kan kujerar
  • Alamu sun nuna cewa ya ɗauki matakin ne biyo bayan rashin gamsuwa da mutanen da aka zaɓo domin zama ministoci a sabuwar gwamnatin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kasar Iran - Mataimakin shugaban ƙasan Iran Mohammed Javad Zarif ya yi murabus daga muƙaminsa.

Mohammed Javad Zarif ya yi murabus ne daga cikin gwamnatin shugaban ƙasa Massud Pezeshkian kwanaki 11 bayan hawansa mulki.

Mataimakin shugaban kasan Iran ya yi murabus
Mohammed Javad Zarif ya yi murabus daga mukaminsa Hoto: @JZarif
Asali: Twitter

Meyasa ya yi Mohammed Zarif ya yi murabus?

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya sanar da murabus ɗin nasa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban gamsu da aikina ba kuma na yi nadama cewa na kasa sauke nauyin da ake buƙata daga gare ni."

- Mohammed Javad Zarif

An danganta murabus ɗin ne da rashin gamsuwa da mutanen da aka zaɓi domin zama ministocin sabuwar majalisar ministocin Pezeshkian.

Mohammed Zarif ya nuna alamun cewa aƙalla bakwai daga cikin ministoci 19 da aka naɗa ba su yake so ba, wanda hakan ya taimaka wajen yanke shawarar murabus ɗinsa.

Iran na fuskantar ƙalubale

Wannan shine babban ƙalubale na biyu ga Shugaba Pezeshkian tun bayan da ya hau kan karagar mulki a ƙarshen watan Yuli.

Batu na farko ya shafi kisan da aka yiwa shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a birnin Tehran.

Zarif wanda babban jigo ne a yaƙin neman zaɓen Pezeshkian, ana sa ran zai taimaka wajen jagorantar aiwatar da sauye-sauye da sabuwar manufa kan hulɗa da ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo ya fadi hanyar da Najeriya za ta samu ci gaba

Sai dai jerin sunayen majalisar ministocin da Pezeshkian ya gabatar bai yi daidai da shirin kawo tsare-tsaren ba, wanda ke nuna yiwuwar yin katsalandan daga ɓangarorin masu tsattsauran ra'ayi na Iran.

Shugaban Iran ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya rasa ransa a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2024.

Hatsarin jirgin wanda ya ritsa da wasu jami'an gwamnatin ƙasar ya yi sanadiyyar rasuwar dukkanin mutanen da ke cikin jirgin mai saukar ungulu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng