Ba a Gama da Maganar Zanga Zanga ba, Tinubu Ya Tura Sako ga Nijar da Burkina Faso

Ba a Gama da Maganar Zanga Zanga ba, Tinubu Ya Tura Sako ga Nijar da Burkina Faso

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa za su cigaba da zama da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso domin dawowa ECOWAS
  • Tinubu ya ce abin takaici ne kasashe har guda uku su fice daga kungiyar musamman a lokacin da yake jagorancinta
  • Shugaban ya ce za su tabbatar da samar da tsaro a yankunansu da kuma bin tsarin mulki kasashen da ke cikin kungiyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan tuntubar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso domin dawowa kungiyar ECOWAS.

Tinubu ya ce ECOWAS za ta cigaba da kokarin shawo kan kasashen domin su dawo a daura daga inda aka tsaya.

Kara karanta wannan

Dattawan Kudu sun raba gari da Tinubu kan kalamansa, siyasarsa ta samu koma baya

Tinubu ya sha alwashin shawo kan Nijar da Mali da Burkina Faso dawowa ECOWAS
Bola Tinubu ya ce za su cigaba da kiran Mali da Nijar dawowa ECOWAS. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya bukaci dawowar Nijar, Mali ECOWAS

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 a Abuja yayin ganawa da hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce za su cigaba da samar da tsaro a yankunan kasashen da kuma bin kundin tsarin mulki, Premium Times ta tattaro.

Shugaban da ke jagorantar ƙungiyar ya ce ya fuskanci kalubale ganin cewa a lokacinsa kasashe uku suka fita daga ECOWAS.

ECOWAS: Bola Tinubu zai samar da tsaro

"Mun saka a ranmu za mu samar da tsaro a yankunanmu da kuma tabbatar da bin dokar tsarin mulki."
"Kalubale ne a gare ni lokacin wa'adina kasashe uku sun fita daga ECOWAS."
"Za mu yi duk mai yiwuwa domin shawo kansu su dawo wannan ƙungiya."

- Bola Tinubu

Hakan na zuwa ne yayin da matasan Najeriya ke zanga-zanga kan halin kunci da matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

Zanga-zanga: Amurka da Burtaniya sun tsoma baki

Kun ji cewa kasashen Amurka da Burtaniya sun yi martani kan halin da ake ciki a Najeriya game da zanga-zangar halin kunci.

Kasashen biyu sun yaba da manufofin Bola Tinubu inda suka bukaci ya tattauna da matasa domin shawo kan matsalolin da ake ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa suka cika titunan kasar domin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.