Chevening 2025/26: Yadda Ɗaliban Najeriya Za Su Nemi Tallafin Karatu a Ƙasar Birtaniya

Chevening 2025/26: Yadda Ɗaliban Najeriya Za Su Nemi Tallafin Karatu a Ƙasar Birtaniya

  • An bude gurbin neman tallafin karatu na Chevening da ke a Birtaniya ga daliban da ke sha'awar neman tallafin a zangon karatu na 2025/2026
  • Tuni aka bude shafin da dalibai za su nemi tallafin yin karatu a babbar jami'a a Birtaniya kuma za a rufe neman tallafin ne zuwa 5 ga Nuwamba, 2024
  • A zantawarmu da Dakta Attahiru Dan-Ali Mustapha, wanda ya taba cin gajiyar makamancin wannan tallafi, ya yi magana karin haske

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Birtaniya - An bude gurbin neman tallafin karatu na Chevening na zangon 2025/2026 wanda aka ba dalibai damar neman tallafin daga yanzu har zuwa 5 ga Nuwamban 2024.

Kara karanta wannan

Kowa ya rasa: Tinubu ya dakatar da siyar da shinkafar N40,000 ga 'yan Najeriya

Chevening tana ba da tallafin karatu ga daliban da suka cancanta su yi karatu a Birtaniya na tsawon shekara guda kyauta, amma ga wadanda za su yi digiri na biyu.

Kasar Birtaniya ta bude kofa ga dalibai su nemi tallafin karatu a zangon 2025/2026
Za a rufe neman tallafin karatu na Chevening a ranar 5 ga watan Nuwamba. Hoto: @CheveningFCDO
Asali: Twitter

A cewar wani rahoto daga shafin yanar gizo na Chevening, ofishin da ke kula da diflomasiyya da harkokin wajen Birtaniya (FCDO) tare da wasu kungiyoyi ne suka dauki nauyin ba da tallafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, an sanar da bude kofar neman tallafin karatun a shafinta na X, @CheveningFCDO ranar Talata, 6 ga watan Agusta.

Yadda dalibai za su nemi tallafin Chevening

  • Dole ne daliban da za su nemi tallafin ya kasance sun cika waɗannan sharuddan:
  • Ka kasance dan asalalin kasa ko shiyyar da Chevening ke ba tallafin karatu.
  • Ba da tabbacin komawa kasarka akalla shekaru biyu bayan wa'adin tallafinka ya kare.
  • Ka kasance kana da akalla kwarewar aiki ta shekaru biyu (awa 2,800).
  • Ka kasance kana da sakamakon digirin farko da zai iya baka damar yin digiri na biyu a Birtaniya
  • Ka nemi gurbin karatu a jami'o'i uku da na Birtaniya da aka amince da su

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta fitar da makudai a watanni 6, an batar da Naira tiriliyan 1

Dole ne dalibin ya kasance ya samu takardar ba shi gurbin karatu daga cikin jami'o'in da ya nema, kuma dole ya kiyaye wa'adin samun gurbin karatun kamar yadda yake a shaidar ba shi gurbin.

Damar yin karatu kyauta a Birtaniya

Samun tallafin karatu na Chevening na nufin cewa dalibi zai yi karatu a Birtaniya ba tare da ya biya ko sisin kwabo ba. Ga abubuwan da tallafin ya kunsa:

  • Kudin makaranta
  • Alawus na wata wata.
  • Biyan kudin jirgi daga kasar dalibi zuwa Birtaniya da kuma komawarsa bayan kammala karatu.
  • Alawus na 'maraba da zuwa' (idan dalibi ya isa Birtaniya).
  • Alawus na 'Sauka lafiya' (idan dalibi zai koma gida).
  • Kudin biza
  • Kudin zuwa halartar tarurrukan Chevening da ake yi a Birtaniya

Wanda ya taba cin gajiya ya magantu

A zantawarmu da wani Dakta Attahiru Dan-Ali Mustapha, wanda ya taba cin gajiyar makamancin wannan tallafin, ya ce babu kamun kafa ko sanayya a neman tallafin karatu a kasar waje.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Tinubu ya fadi yadda za a ci gajiyar shinkafar N40,000, ya saka ka'ida

Dakta Attahiru ya ce lokacin da ya nemi tallafin, bai bi ta hanyar kowa ba, ya cike dukkanin abubuwan da ake bukata, kuma ya tattauna da su, a karshe Allah ya sa ya samu.

"Neman tallafin karatu a kasar waje na da matukar wahala, amma idan aka jajurce ana samu. Mutum ya zama ya fara hada takardun da ake bukata kuma ya cike sharuddan makarantu.
"Kadan daga ciki shi ne mutum ya tanadi bayanin sakamakon digirinsa na farko, ya samu shaida daga malamai da wurin da ya taba aiki, da kuma takardar shaidar iya turanci da sauransu."

- A cewar Dakta Attahiru.

An damfari masu neman aiki a Birtaniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da 'yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), ta ce sama da ‘yan Najeriya 1,000 ne aka damfara da sunan nema masu guraben ayyukan yi a Burtaniya.

Hukumar ta bayyana cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun yi asarar kusan dala 10,000 a kokarinsu na neman samun ayyukan yi a kasashen waje.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.