Zaben Amurka: Abubuwa 4 da Ya Kamata a Sani kan Tim Walz, Mataimakin Kamala Harris

Zaben Amurka: Abubuwa 4 da Ya Kamata a Sani kan Tim Walz, Mataimakin Kamala Harris

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Amurka - Mataimakiyar shugaban ƙasan Amurka Kamala Harris ta zaɓi gwamnan jihar Minnesota, Gwamna Tim Walz a matsayin abokin takararta a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamban 2024.

Kamala Harris ta zama ƴar takarar shugaban ƙasan Amurka ta jam'iyyar Democrat bayan Shugaba Joe Biden ya janye daga takara.

Tim Walz ya zama mataimakin Kamala Harris
Kamala Harris ta zabi Tim Walz a matsayin mataimakinta Hoto: Demetrius Freeman/The Washington Post and Stephen Maturen
Asali: Getty Images

Kamala Harris ta zabi abokin takara

Wasu majiyoyi sun sanarwa jaridar CBS News cewa Kamala Harris ta zaɓi Tim Walz a matsayin abokin takararta ne a ranar Talata, 6 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaɓo Tim Walz a matsayin abokin takararta na zuwa ne yayin da take ƙoƙarin ganin ta yi nasara a kan Donald Trump na jam'iyyar Republican a zaɓen shugaban ƙasan na watan Nuwamban 2024.

Kara karanta wannan

Wani malamin addini ya gayawa Tinubu gaskiya, ya fadi babbar matsalar gwamnatinsa

Abubuwan sani dangane da Tim Walz

Jaridar ABC News ta tattaro wasu abubuwan sani dangane da gwamnan na jihar Minnesota wanda zai yiwa Kamala Harris mataimaki.

Tasowarsa Tim Walz a Amurka

Tim Walz mai shekara 60 a duniya, ya taso ne a wani ƙaramin ƙauye mai suna West Point da ke a Nebraska.

Ya kammala digirinsa na farko a shekarar 1989 a kwalejin Chadron da ke Nebraska.

Ya yi aikin koyarwa a Mankato da ke jihar Minnesota inda a nan ne ya haɗu da matarsa wacce ya aura.

Tim Walz ya shiga aikin soja inda ya yi ritaya a shekarar 2005 bayan ya kwashe shekara 24 yana hidimtawa ƙasarsa.

Shiga siyasar Walz bayan aikin soja

Tim Walz ya tsunduma cikin harkar siyasa a shekarar 2006 inda ya lashe kujerar ɗan majalisa.

Ya sake lashe zaɓen kujerar ɗan majalisa har sau biyar. A shekarar 2018 ya lashe zaɓen gwamnan jihar Minnesota, kujerar da ya ƙara lashewa a zaɓen shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta faɗi wasu manyan ƙusoshin gwamnati da hannu a zanga zanga

Tim Walz na goyon bayan Biden

Tim Walz ya kasance na gaba-gaba cikin masu nuna goyon baya ga Joe Biden yayin da yake yaƙin zaɓen neman yin tazarce a kujerar shugaban ƙasan Amurka.

Iyalan Tim Walz

Tim Walz yana auren mace ɗaya watau Gwen Walz inda suke da yara biyu waɗanda suka haifa.

Rahoton CNN ya nuna cewa aurensa da Gwen Walz da aka yi a 1994 ya yi sanadiyyar samun Hope Walz, Gus Walz

Karanta wasu labaran kan siyasar Amurka

Donald Trump ya yi barazana kan zaɓen Amurka

A wani labarin kuma, kun ji tsohon shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump ya yi iƙirarin za a yi wani babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya idan bai ci zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake dasa bam, ya hallaka babban jami'in gwammnati a Borno

Donald Trump ya kuma cewa akwai yiwuwar za a yi "yaƙin duniya na uku" idan bai koma kan kujerar mulkin ƙasar Amurka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng