Zanga Zanga Ta Samu Goyon Baya Daga Amurka, An Gargadi Tinubu Kan Taɓa Matasa

Zanga Zanga Ta Samu Goyon Baya Daga Amurka, An Gargadi Tinubu Kan Taɓa Matasa

  • Matasa masu shirin yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun samu goyon baya daga kasar Amurka
  • Kungiyar dimokuraɗiyya ta NADECO a kasar Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya kan yunkurin dakile masu zanga zanga
  • NADECO ta bayyana cewa zanga zangar lumana na cikin yancin dan Adam da majalisar dinkin duniya ta tabbatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Yayin da ake shirin zanga zanga a Najeriya, kungiyar NADECO daga Amurka ta tura sako ga gwamnatin Najeriya.

Kungiyar ta reshen Amurka ta gargadi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan nisantar dakile masu zanga zangar lumana.

Shugaba Tinubu
NADECO ta gargadi Bola Tinubu kan zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa NADECO ta yi kira ga kasashen duniya su sa ido kan yadda zanga zangar za ta gudana.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga zanga: Sakon NADECO ga gwamnati

Shugaban kungiyar NADECO reshen Amurka, Dakta Llyod Ukwu ya bayyana cewa suna goyon bayan zanga zangar lumana a Najeriya.

Dakta Llyod Ukwu ya ce ta hanyar zanga zanga ana samar da canji a mulkin dimokuraɗiyya kuma dokar majalisar dinkin duniya ta tabbatar da ita.

Saboda haka yace yunkurin dakile matasan ba zai haifar da ɗa mai ido ga gwamnatin Najeriya da dimokuraɗiyya ba.

NADECO: 'Tinubu ma ya yi zanga zanga'

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar NADECO ta ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ma ya ci albarkacin zanga zanga da suka gudana a shekarun baya.

NADECO ta ce a shekarar 2014 Bola Tinubu da manyan yan Najeriya da suka hada da Farfesa Wole Soyinka, Fasto Tunde Bakare da Fasto Adeboye duk sun yi zanga zanga.

Saboda haka kungiyar ta ce zai zama munafurci a ce za a dakile masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Tun kafin fara zanga zanga, an yi baram baram tsakanin jagorori da shugaban 'yan sanda

Yan sanda sun tattauna da 'yan zanga-zanga

A wani rahoton, kun ji cewa a jiya Talata, 30 ga watan Yuli aka yi zama ta yanar gizo tsakanin jagororin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da yan sanda.

Tattaunawar ta kasance ne domin samo hanyar da za a samu zaman lafiya a lokacin zanga zangar saboda kaucewa tarzoma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng