Donald Trump Ya Tada Hankalin Duniya, Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Bai Ci Zabe Ba
- Tsohon shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump ya yi iƙirarin cewa duniya za ta fuskanci yaƙi idan bai lashe zaɓen watan Nuwamba da ke tafe ba
- Donalɗ Trump ya bayyana cewa ana dab da yaƙin duniya na uku idan bai koma kan mulkin ƙasar Amurka ba
- Kalaman na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da faɗa a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'ila da Hamas
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Amurka - Tsohon shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump ya yi iƙirarin cewa za a yi wani babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya idan bai ci zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba mai zuwa ba.
Donald Trump ya kuma cewa akwai yiwuwar za a yi "yaƙin duniya na uku" idan bai koma kan kujerar mulkin ƙasar Amurka ba.
Trump ya gana da Netanyahu
Trump ya bayyyana hakan ne bayan ya gana da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a gidansa da ke Mar-a-Lago a birnin Florida, ranar Juma'a, cewar rahoton VOA News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar ta su na zuwa ne kwana ɗaya bayan Netanyahu ya gana a fadar White House da Shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris, rahoton Hindustan Times ya tabbatar.
"Idan muka yi nasara, zai zama da sauƙi. Komai zai yi aiki kuma cikin sauri. Idan ba mu yi ba, za ku ƙare da manyan yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya da wataƙila yakin duniya na uku."
"Kuna kusa da yaƙin duniya na uku fiye da kowane lokaci tun bayan yaƙin duniya na biyu.
"Ba a taɓa samun lokacin da ya yi kusa da hakan ba, saboda muna da mutanen da ba su da ƙwarewa suna mulkar ƙasarmu."
- Donald Trump
Trump ya saba barazanar yin yaƙin duniya
A baya dai tsohon shugaban ya ce duniya na dab da sake ganin ɓarkewar yaƙin duniya saboda faɗan da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.
Trump ya kuma yi hasashe mai muni game da abin da ka iya faruwa idan bai yi nasarar sake komawa fadar White House ba, ciki har da iƙirarin cewa kasuwar hannayen jari za ta fadi.
Karanta wasu labaran kan Donald Trump
- Bayan kama Donald Trump da laifuffuka, shin zai iya takarar Shugaban kasar Amurka?
- Ana dab da zabe: An harbi tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a wani taro a Pennsylvania
- Donald Trump ya mayar da martani bayan an harbe shi a kamfe, an gano maharbin
Bayanai kan wanda ya harbi Donald Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta bayyana sunan Thomas Matthew Crooks a matsayin wanda ya kai hari a yunkurin kashe tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Matashin da ake zargi da yunƙurin kashe Trump, mai shekaru 20 dan jam'iyyar Republican kamar yadda bayanan zabensa suka nuna. Read more:
Asali: Legit.ng