An Karfafi Masu Zanga Zanga a Najeriya Yayin da Kotu Ta Ba Matasan Kenya Nasara

An Karfafi Masu Zanga Zanga a Najeriya Yayin da Kotu Ta Ba Matasan Kenya Nasara

  • Babbar kotun kasar Kenya ta yanke hukunci a kan hana zanga zanga da rundunar yan sandan kasar ta yi a cikin wannan makon
  • Haka zalika bayan yanke hukuncin, babbar kotun ta ba rundunar yan sandan kasar Kenya sabon umurni da za ta aikata da gaggawa
  • Rundunar yan sandan Kenya ta haramta zanga zangar da ta barke a kasar ne bisa wasu dalilai da ta bayyana da ke da alaka da tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Kenya - Babbar kotun kasar Kenya ta soke matakin da yan sandar kasar suka dauka na hana matasa zanga zanga.

Zanga zanga ta barke a kasar Kenya ne biyo bayan tsananin tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Adawa da Tinubu: Gwamnati ta gano wadanda ke daukar nauyin matasa su yi zanga zanga

Kasar Kenya
Kotu ta ba masu zanga zanga nasara a Kenya. Hoto: Witthaya Prasongsin
Asali: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa kotun ta soke umurnin yan sandan ne duk da cewa za ta cigaba da suararon karar a gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin hana zanga zanga a Kenya

Rundunar yan sanda a Kenya ta hana matasa zanga zanga ne bisa yadda lamarin ya rincabe daga zanga zangar lumana.

Rundunar yan sanda ta ce ta dauki matakin ne biyo bayan samun kashe kashe da kone kone a cikin zanga zangar, rahoton Daily Trust.

Kotu da dakatar da yan sandan Kenya

Sai dai bayan matakin da yan sanda suka dauka, babbar kotun kasar ta ce hakan ya saɓa hakkin yan kasa na yin zanga-zanga.

Alkalin kotun, mai shari'a, Bahati Mwamuye a ranar Alhamis ya yarda a cigaba da zanga zanga a halin yanzu duk da cewa kotun za ta kara zama domin duba lamarin.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan wanda ya kai hari masallaci ana asuba

Zanga zanga: Kotu ta umurci yan sanda

Babbar kotun ta umurci sufeton yan sandan kasar Kenya, Douglas Kanja Kirocho ya yada umurnin da ta bayar.

Kotun ta kara da cewa Douglas Kanja Kirocho ya tabbatar da cewa umurnin kotun ya isa wajen dukkan jami'an yan sanda a fadin ƙasar.

Abuja: Yan sanda sun hana zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakile yunkurin kungiyar ma'aikatan manyan makarantu na gudanar da zanga zanga a Abuja.

Kungiyar ma'aikatan SSANU da NASU sun shirya gudanar da zanga zanga a jiya Alhamis domin nuna fushinsu saboda an hana su albashin watanni hudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng