Zanga Zanga Ta Tsananta: Shugaban Ƙasa Ya Kori Ɗaukacin Ministocinsa Ya Bar Mutum 1

Zanga Zanga Ta Tsananta: Shugaban Ƙasa Ya Kori Ɗaukacin Ministocinsa Ya Bar Mutum 1

  • Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya yi jawabi kai tsaye ga al'ummar kasar bayan da ya rusa majalisar ministocinsa baki daya
  • Shugaba Ruto ya kori ministocin ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a fadin kasar na tsawon makonni
  • Wadanda wannan korar ba ta shafa ba sun hada da sakataren gwamnatin kasar da ministan harkokin wajen kasar, Musalia Mudavadi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kenya - A ranar Alhamis, shugaban kasar Kenya, William Ruto ya sallami daukacin majalisar ministocinsa baya amma ya kyale ministan harkokin wajen kasar.

An ruwaito cewa Shugaba William Ruto ya kori ministocin ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a fadin kasar na tsawon makonni.

Kara karanta wannan

"Hakurin talaka ya fara karewa": Sanatoci sun ankarar da Tinubu kan yunwa a kasa

Shugaba William Ruto na Kenya ya yi jawabi kai tsaye ga 'yan kasarsa
Shugaban kasar Kenya ya sanar da korar daukacin ministocin gwamnatinsa. Hoto: @WilliamsRuto
Asali: Twitter

Zanga-zanga ta tsananta a kasar Kenya

Zanga-zangar da matasa ke jagoranta, wadda ta samo asali daga wani yunkuri na karin haraji a kasar, ya haifar da rikicin shugabanci mafi muni ga Shugaba Ruto, inji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akalla mutane 39 ne aka kashe a arangamar da suka yi da ‘yan sanda yayin da wasu masu zanga-zangar suka yi kutse a gunun majalisar kasar tare da lalata kayayyaki a watan jiya.

A yayin gabatar da wani jawabin kai tsaye, Shugaba Ruto ya kuma sanar da cewa ya kori babban mai shigar da kara na kasar amma korar ba ta shafi ofishin mataimakin shugaban kasar ba.

Shugaba Ruto ya kori daukacin ministocinsa

Kamar yadda kafar labaran DW ta ruwaito, Shugaba Ruto ya sanar da 'yan kasar cewa:

“A yau na yanke shawarar sallamar daukacin majalisar ministocina tare da babban lauyan gwamnatin kasar Kenya nan take.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikatar tarayya, ya kafa kwamitin kiwon dabbobi

"Na dauki wannan matakin ne bisa ga ikon da doka ta 1521 da ta 1525 B na kundin tsarin mulkin kasar ta ba ni da kuma sashe na 12 na dokar babban lauyan gwamnati."

Wadanda za su ci gaba da kasancewa a kan mukamansu sun hada da sakataren gwamnatin kasar da ministan harkokin wajen kasar Musalia Mudavadi da mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua.

Shugaba Tinubu ya kori ministar jin kai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kori ministar harkokin jin kai da yaki da talauci, Dakta Betta Edu ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Tinubu ya ce dakatarwar wani ɓangare ne na alwashin da ya ɗauka na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkomin tafiyar da mulkin al’ummar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.