An Tura Dan TikTok Zuwa Gidan Yari Saboda Zagin Shugaban Kasa

An Tura Dan TikTok Zuwa Gidan Yari Saboda Zagin Shugaban Kasa

  • Kotu ta yankewa wani ɗan ƙasar Uganda, Edward Awebwa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa samunsa da laifin zagin shugaban ƙasar, Yoweri Museveni da iyalansa a wani faifan bidiyo na TikTok
  • Edward Awebwa mai shekara 24 a duniya ya amsa laifin yin kalaman ƙiyayya da yada labaran ƙarya, amma bai nuna nadama a gaban kotu ba
  • Hukuncin dai ya janyo damuwa daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama, waɗanda ke zargin cewa ya keta ƴancin faɗin albarkacin baki, kuma wani yunƙuri ne na murkushe masu caccakar gwamnati a Uganda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Uganda - Wata kotu a Uganda ta yankewa Edward Awebwa mai shekaru 24 hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifin zagin shugaban ƙasar Yoweri Museveni.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega sabon mukami

Ana kuma zarginsa da zagin uwargidan shugaban ƙasar, Janet Museveni, da ɗansu Muhoozi Kainerugaba a wani bidiyo da ya yi a TikTok.

Kotu ta daure dan TikTok a Uganda
Matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. (An yi amfani da hoton ne kawai domin misali)
Asali: Getty Images

Edward Awebwa ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su na kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya ciki har da iƙirarin cewa haraji zai ƙaru a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Museveni, cewar rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotu ta kulle ɗan TikTok a Uganda?

Mai shari'a Stella Maris Amabilis, ta amince da neman yafiya da Awebwa ya yi, amma ta lura cewa bai nuna nadamar abin da ya aikata ba, kuma ya yi amfani da kalaman ɓatanci a faifan bidiyon.

Hukuncin na da nufin koyar da Edward Awebwa darasi da kuma mutunta shugaban ƙasa, uwargidan shugaban ƙasa, da kuma ɗansa na farko.

Hukuncin ya janyo cece-kuce

Hukuncin ya jawo ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun nuna damuwa, waɗanda suka daɗe suna zargin mahukunta a Uganda da take ƴancin faɗar albarkacin baki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta jawo hankalin Tinubu kan yunwa a kasa, ta ba shi mafita

Irin hakan ya taɓa faruwa ga wani marubuci Kakwenza Rukirabashaija, wanda ya arce zuwa ƙasar Jamus bayan an tuhume shi da yaɗa kalamai masu tsauri.

Haka kuma an taɓa kulle wata ƴar gwagwarmaya mai suna Stella Nyanzi, a gidan kurkuku saboda wallafa wata waƙa.

Hadimi ya magantu kan sukar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Buhari, Femi Adesina ya bayyana yadda ya bar zuwa coci saboda Fasto ya soki mulkin Buhari.

Adesina ya ce tuni ya dauke kafa a cocin Foursquare da ke Abuja saboda sukar Buhari da Fasto Babajide Olowodola ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng