Rikicin Duniya: An Kama Mutumin da Ya Ɓoye Macizai Sama da 100 a Wandonsa

Rikicin Duniya: An Kama Mutumin da Ya Ɓoye Macizai Sama da 100 a Wandonsa

  • Jami'an hukumar kwastam a kasar Sin sun kama wani matashi ya cusa macizai a wandonsa yana shirin safararsu
  • Hukumar kwastam ta bayyana cewa mutumin ya saba doka ta inda ya dauki aniyar yin fatauci ta haramtacciyar hanya
  • Har ila yau, hukumar ta kuma bayyana mataki na gaba da za ta dauka a kansa bayan hukumomi sun kammala bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Jami'an hukumar kwastam a kasar Sin sun cafke wani mutum na kokarin safarar macizai ta barauniyar hanya.

Hukumomin kasar Sin sun tabbatar da cewa mutumin ya ɓoye tarin macizan ne a cikin wandonsa.

Kasar Sin
An kama mai safarar macizai a Sin. Hoto: TheFeedski
Asali: Facebook

Jami'an hukumar kwastam ne suka tare mutumin suna bincikensa kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kama rubabbun kaji da lalatatun magunguna ana shirin shigowa da su Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama mai safarar macizai

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya fito ne daga garin Hong Kong yana neman tsallakawa zuwa Shenzhen.

A kokarin tsallaka boda ne sai jami'an kwastam suka bincike shi suka ga tarin macizai a wandonsa, rahoton The Economics Times.

Yadda mutumin ya ɓoye macizan

Hukumar kwastam ta bayyana cewa mutumin ya ɓoye macizan ne a cikin ledodi guda shida ya sanya su cikin aljihun wandonsa.

Ta kuma bayyana cewa yayin da ta bude ledodin ta samu nau'ukan macizai da dama wanda yawansu ya kai 104.

Matakin da kasar Sin za ta dauka

Kasar Sin ta haramta shigo da nau'ukan macizai da babu su a fadin ƙasar sai da izini amma mutumin ya karya dokar.

Duk da cewa hukumar kwastam ba ta ayyana hukuncin da za a yiwa mutumin ba, ta ce za a masa hukunci daidai da doka saboda ya aikata laifi.

Kara karanta wannan

Hukumar NERC ta lissafa kayan lantarki da ya kamata a rika ba yan Najeriya kyauta

Dan kasar Sin ya kashe budurwa

A wani rahoton, kun ji cewa wata matashiya 'yar jihar Abia ta mutu bayan da wani dan kasar Sin da ake zargi ya tunkudo ta kasa daga saman babbar mota.

Ana zargin cewa dan Sin, wanda ke aiki a kamfanin Inner Galaxy ya kashe Ocheze Ogbonna ne saboda kin amincewa da soyayyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng