Jam’iyyar Labour Ta Karbe Mulkin Birtaniya, Keir Starmer Ya Zama Sabon Firaminista

Jam’iyyar Labour Ta Karbe Mulkin Birtaniya, Keir Starmer Ya Zama Sabon Firaminista

  • Jam'iyyar Labour a Birtaniya ta yi nasarar samun kujeru mafin rinjaye a House of Commons, inda a yanzu za ta samar da firaminista
  • Keir Starmer, dan takara a jami'iyyar Labour shi ne za a rantsar matsayin sabon firaminista bayan fitar sakamakon zaben
  • Rishi Sunak, dan takarar firaminista na jam'iyyar Conservative, ya rungumin kayen da ya shatare da taya Keir Starmer murna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Burtaniya - Keir Starmer, dan takarar jam'iyyar adawa ta Labour, ya yi nasara a babban zaben Birtaniya kuma shi ne zai zama firaminista na gaba.

Jam'iyyar adawa ta Labour ta yi nasarar samun kujeru 326 na majalisar da ake bukata.

Ingila tayi sabon firayim minista. Hoto daga @Keir_Starmer
Ingila Tayi Sabon Firayim Minista, Sunak Ya Taya Shi Murnar Nasara a Zabe
Asali: Twitter

Firaminista Rishi ya karbi kaddara a Birtaniya

Kara karanta wannan

Shinkafi ya fadi abin da ke kawo rashin tsaro a Arewa maso Yamma, ya ba da mafita

Al Jazeera ta ce firaminista mai barin gado, Rishi Sunak, ya rungumi kayen da ya sha inda ya dauki alhakin faduwar jam'iyyarsa ta Conservative.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rishi Sunak ya bayyana godiyarsa ga jama'ar mazabarsa tare da taya Keir Starmer murna kan nasarar da ya samu.

Ya ce zai mika mulki cikin lumana tare da fatan alheri a kowanne bangare. Sunak ya baiwa sauran 'yan jam'iyyarsa da suka fadi hakuri.

Yadda zaben Birtaniya ya gudana

Rahoton BBC ya nuna cewa zuwa yanzu an bayyana kusan dukkanin sakamakon zaben, ana hasashen jam'iyyar Labour za ta kafa gwamnati mai zuwa, tare da mafi yawan 'yan majalisu.

An ruwaito kasar Birtaniya ta yi babban zabenta a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli inda miliyoyin jama'a suka kada kuri'ar zaben 'yan majalisa.

'Yan majalisar da aka zaba a yanzu, za su wakilci mazabunsu da mutanensu a babbar majalisar Birtaniya ta House of Commons.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi a shirye yake, zai karɓi kowacce dokar gwamnatin Sokoto

Yadda zauren majalisar Birtaniya yake

Mazabun Birtaniya sun kasu har zuwa 650, inda kowacce maza ta zabi dan majalisa daya domin wakiltarta.

Yayin da yawancin 'yan takarar na wakiltar jam'iyyar siyasa, wasu kuma sun yi takara ne ba tare da jam'iyya ba.

Zaben yana da daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a jadawalin siyasar Birtaniya.

An ce zaben ya gyara akalar makomar siyasar kasar tare da bayyana shugabannin da zasu dinga yanke muhimman hukunci a madadin 'yan kasa.

'Yan kwangila 39 za su fuskanci majalisa

A wani labari na daban, an ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta fusata da wasu 'yan kwangila 39 da suka karba kudi suka ki fara aiki.

Ministan ayyuka, David Umahi, ya sanar da cewa zasu tuhumesu kuma su yi amfani da EFCC wurin karbo kudin gwamnati da suka makale.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel