Ingila ta yi wa Najeriya mugun baki, ta ce rikici zai iya barkewa a kasar kafin zaben 2023

Ingila ta yi wa Najeriya mugun baki, ta ce rikici zai iya barkewa a kasar kafin zaben 2023

  • Foreign Commonwealth and Development Office ta koka da halin da Najeriya ta ke ciki
  • Christopher Pycroft ya bayyana cewa babu wani yanki da ba a rikici yanzu a kasar nan
  • Hukumar cigaban kasashen renon Birtaniya ta ce za a iya samun matsala a zaben 2023

Wani babban darekta a ofishin cigaban kasashen renon Birtaniya, Foreign, Commonwealth and Development Office, ya yi magana game da zaben 2023.

Christopher Pycroft ya bayyana cewa rikicin da ake fama da su a jihohin Najeriya, za su iya jawo wa tsarin damukaradiyyar kasar nan cikas a zabe mai zuwa.

The Cable ta ce Christopher Pycroft ya bayyana wannan ne ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2021, wajen kaddamar da shirin PISI da gwamnoni su ka fito da shi.

KU KARANTA: Ba a Ingila aka yi ram da Nnmadi Kanu ba - Kasar Birtaniya

Kungiyar gwamnonin jihohn Najeriya watau NGF, ta hada kai da hukumar FCDO ta Birtaniya, ta kawo wannan tsarin da zai wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.

Mista Pycroft ya na ganin raunin bangaren shari’a da kama-karyar da ake yi a kasar nan ne yake kara ta’azzara duk rigingimun da ake fama da su yanzu a Najeriya.

Darektan na Foreign, Commonwealth and Development Office ya bayyana shigowar makamai da rikicin da ake yi a kafafen sadarwa a matsayin barazana ga kasar.

Jaridar ta rahoto Baturen ya na cewa yadda za a magance matsalolin shi ne a rika sauraron koken al’umma.

KU KARANTA: Nnamdi Kanu: Majalisar Ingila za ta binciki Gwamnatin Tarayya

APC ta na kamfe a 2019
Shugaban Najeriya wajen kamfe Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Ana rikici a yankin Arewa da kudancin Najeriya

“Yawan rigingimun da ake yi zai iya hargitsa tsarin damukaradiyyar Najeriya kafin zaben 2023.”
“Ana fama da ‘yan ta’adda a Arewa maso gabas, rikicin makiya da manoma ya ratsa sauran jihohi, mutanen Neja-Delta suna rigima a kan arzikin kasarsu.”
“Babu zaman lafiya a yannkin Kudu maso gabas, ga garkuwa da mutane a Arewa ta yamma.”

Pycroft ya bada shawara cewa tura ‘yan sanda da sojoji kadai ba zai shawo kan matsalolin ba, ya yi kira ga gwamnati ta yi wa kowa adalci domin a zauna lafiya.

A safiyar Juma'a ne rahoto ya zo mana cewa Amurka, Ingila, Faransa da sauran 'Yan G7 za su yi karo-karo, su ba Najeriya gudumuwa kusan Naira biliyan 190.

Jakadar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing ta ce mutane miliyan 8.7 da doriya ne su ke bukatar a kawo masu dauki a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel