Fusatattun Matasa Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta, Bayanai Sun Fito

Fusatattun Matasa Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta, Bayanai Sun Fito

  • Wasu fusatattun matasa a ranar Laraba 3 ga watan Yuli sun kai hari wani ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa INEC tare da ƙona shi a jihar Benue
  • Matasan da ke zanga-zangar nuna adawa da hare-haren ƴan bindiga sun ƙona ofishin INEC da ke Sankara, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum
  • Kwamishinan INEC a birnin Abuja, Sam Olumekun, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tare da bayyana abin da ya faru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu fusatattun matasa sun ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Benue.

Matasan waɗanda suka fito zanga-zanga kan hare-haren ƴan bindiga sun ƙona ofishin na INEC ne da ke a Sankara, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar zaman gida ta tsawon sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Ukum

Matasa sun kona ofishin INEC a Benue
Matasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Benue Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Matasa sun bankawa ofishin INEC wuta

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Sam Olumekun ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sam Olumekun ya ambato Farfesa Sam Egwu, kwamishinan INEC na jihar Benue yana cewa matasan sun mamaye ofishin ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Ya yi nuni da cewa, ko da yake ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnar da aka yiwa ginin tana da yawa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, zanga-zangar ta yi ƙamari inda aka lalata wasu cibiyoyin gwamnati ciki har da ofishin INEC.

Me INEC ta ce kan lamarin?

"Kwamishanan INEC na jihar Benue, Farfesa Sam Egwu ya ruwaito cewa an kai hari ofishinmu na Sankara, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum tare da ƙona shi."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

"Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, an yiwa ginin ɓarna sosai. An lalata kayan ofis da sauran kayayyaki da suka haɗa da janaretoci guda 10, akwatunan zaɓe guda 300, da rumfar kaɗa ƙuri’a guda 270 a harin.”

- Sam Olumekun

A halin da ake ciki, Gwamna Hyacinth Alia ya ayyana dokar hana fita a ƙaramar hukumar Ukum sakamakon zanga-zangar da aka yi.

INEC ta faɗi shirin zaben gwamnan Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa 19 ne za su fafata a zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kwamishinar zaɓe ta jihar, Misis Oluwatoyin Babalola, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da wakilan jam'iyyun siyasa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel