An Naɗa Sabon Mai Rike Makullin Ɗakin Ka’aba, Ya Yi Alkawari ga Al’ummar Musulmi
- A satin da ya wuce ne mai rike da makullin Ka'aba na 109 a tarihin, Sheikh Saleh Al-Shaibi ya kwanta dama a kasar Saudiyya
- Biyo bayan rasuwarsa, an naɗa sabon wanda zai cigaba da rike makullin da kuma yiwa ɗakin Ka'aba hidama daga kabilar Shaiba
- Sabon hadimin, Sheikh Abdulwahab bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi ya yi alkawari ga al'ummar Musulmin duniya baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ƙasar Saudi Arabia - Biyo bayan rasuwar mai rike makullin Ka'aba na 109, Sheikh Saleh Al-Shaibi an naɗa wanda zai cigaba da rike makullin.
Zuriyar Sahabi Usman bin Ɗalha (Allah ya kara masa yarda) sun zaɓi Sheikh Abdulwahab bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi ya rike matsayin.
Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da shafin kasar Saudiyya mai suna Inside the Haramain ya wallafa a yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka naɗa mai rike makullin Ka'aba
A yammacin jiya Litinin ne aka zaɓi Sheikh Abdulwahab Al-Shaibi a matsayin wanda zai cigaba da rike makullin ɗakin Ka'aba.
An zaɓi Sheikh Abdulwahab ne yayin wani taro da ya haɗa hukumomi da zuriyar gidan Banu Shaiba kuma an mika masa makullin Ka'aba yayin taron.
Mikawa Sheikh Abdulwahab makullin na nuni da cewa daga lokacin ya zama wanda zai cigaba da lura da ayyukan ɗakin Ka'aba.
Bayanin mai riƙe da makullin Ka'aba
Sheikh Abdulwahab Al-Shaibi wanda ya kasance mai shekaru 78 a duniya shi ne na 110 cikin jerengiyar masu rike da makullin Ka'aba a tarihi.
Yayin da yake bayyani bayan karɓar aikin ya ce zai cigaba da yin kokari domin kare martabar masallacin Ka'aba mai alfarma.
Sheikh Abdulwahab ya kuma yi alkawarin cewa zai cigaba da aiki wajen yiwa Musulunci hidima ba tare da nuna bambanci ba.
An mayarwa alhazan Kaduna kudi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar manema labaran aikin Hajji mai zaman kanta (IHR) ta tura saƙon jinjina ga hukumar jin daɗin mahajjata ta jihar Kaduna.
Kungiyar IHR ta tura saƙon ne biyo bayan abin kirki da hukumar jin dadin alhazan ta yi na mayarwa mahajjatan jihar Kaduna rarar kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng